Labari mai dadi : Labari da zai Farantawa duk wani Dan kwankwasiyya rai da mai son Abba
Mai bada umurni kuma mataimaki na musamman na mai girma gwamna abba kabir yusuf a fagen Kannywood sunusi oscar 442 inda ya wallafa wani labari mai daɗi ga masoyan engr. Abba Kabir yusuf.
Sususi oscar dai ya kawo wanann labari da wani bayan Allah yake gayamasa cewa yayi wani babban mafarki wanda ya sanya dole ya bashi wannan labari domin tabbas irin yadda ake ciki a garin Kano al’amari ne na tashin hankali akan shari’ar zaben kano da ake daf da yankewa.


Ga abinda yake cewa.
“Yanzu wani mutumina ya kirani awaya yabani wani labari mai faranta rai,
Ina daga wayar yace dani Oscar sunana wane, ance kazo bana nan jiya, nace dashi kwarai da gaske
Yace dani yana hanya yana dawowa daga Mecca ya sake fadamin Oscar naje RAUDAH kuma nayiwa mai girma GOMNA addu’ar samun nasara a kotun koli,
Bayan na kwanta bacci sai nai mafarki da SHUGABAN HALITTA ANNABI MUHAMMADU S.A.W yazo inda muke muna zaune muda yawa, agurin shima mai girma GOMNA na zaune awajen
SHUGABA yana zuwa ya taba bayan mai girma GOMNA, juyowar gomna keda wuya SHUGABAN HALITTA yace dashi ka kwantar da hankalinka ina tareda kai.
Wallahi daya ban wannan labari sai naji duk wani bakin ciki ya yayemini, Allah Alhamdulillah.”