Labarai

Kaduna: Gwamna Uba Sani Ya Caccaki Kalaman Hukumar Rundunar Tsaro ta Ƙasa Kan Dalilin Jefa Bam a Taron Musulmi, Ya Nemi Abu 1

Gwamnan Kaduna ya nuna rashin jin daɗinsa da kalaman hedkwatar tsaro cewa ‘yan bindiga ne suka saje da mutane a kauyen Tudun Biri Malam Uba Sani ya ce wannan magana ba ta dace ba kuma ta nuna rashin kulawar sojoji, inda ya nemi mahukunta su janye ta

A ranar Lahadi da ta gabata, jirgin sojojin Najeriya ya jefa bam har sau biyu kan taron Musulmai a kauyen

Gwamnan jihar Kaduna ya yi fatali da ikirarin hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) cewa sojoji sun yi kuskuren jefa Bam a kauyen Tudun Biri saboda ‘yan ta’adda sun saje da fararen hula.

Jaridar liberty Tvr na ruwaito,Lamarin wanda ya faru a ranar Lahadin da ta gabata, ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 120 tare da jikkata wasu da dama a karamar hukumar Igabi.

Kaduna: Gwamna Uba Sani Ya Caccaki Kalaman Hukumar Rundunar Tsaro ta Ƙasa Kan Dalilin Jefa Bam a Taron Musulmi, Ya Nemi Abu 1
Kaduna: Gwamna Uba Sani Ya Caccaki Kalaman Hukumar Rundunar Tsaro ta Ƙasa Kan Dalilin Jefa Bam a Taron Musulmi, Ya Nemi Abu 1

Amma daraktan yada labarai na DHQ, Edward Buba, ranar Talata, ya ce dalilin da ya sa suka saki bama-baman shi ne ‘yan ta’adda sun shiga cikin jama’ar ƙauyen.

Sani Da yake jawabi a gidan talabijin na Channels TV ranar Jumu’a, Gwamna Uba Sani ya bayyana wannan kalamai na DHQ a matsayin rashin kulawa da sanin aiki. Ya jaddada cewa ya kamata a tantance irin waɗan nan ikirarin gabanin ɗaukar mummunan mataki irin wannan kan mutanen da ba su ji ba kuma ba su gani ba.

Uba Sani ya ce: “Abin da ya auku a kauyen Tudun Biri babu daɗi, amma yadda babban hafsan tsaro ya ɗauki laifin kuskuren da aka yi, shiyasa mutane suka haƙura.” “Amma maganar cewa wai ƴan ta’adda ne suka shiga garin suka saje da mutane abu ne da ke bukatar tantancewa. Ina ganin wannan kalaman babu tunani a cikinsu ko kaɗan.”

Sanata Sani ya ce babu kuskure a harin Kaduna “Idan ka je asibitin da aka kwantar da waɗanda harin bama-baman ya shafa ka ga gaskiyar abin da ya faru, zaka yi tir da wannan kalamai.” Bayan haka Gwamna Sani ya yi kira ga babban hafsan rundunar sojin ƙasa, Janar Lagbaja, ya duba yiwuwar janye wannan magana.

Kungiyar CAN Ta Yi Martani Game da Harin Bam Kan Masu Maulidi a Kaduna

A wani rahoton kuma Yayin da ake jimamin mutuwar masu Maulidi a Kaduna, Kungiyar CAN ta yi Allah wadai da harin bam din da sojoji su ka kai. Shugaban kungiyar, Daniel Okoh shi ya bayyana haka inda ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta fifita kare rayukan al’umma.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button