Labarai

A yiwa Kano adalci ta hanyar tabbatar da abinda al’umma ke muradi – Gamayyar Malamai

Advertisment

Gamayyar Malamai a jihar Kano na bangarorin Tijjaniyya, Ƙadiriyya da kuma Izala, da suka hada da Limamai da Alarammoni sun yi kira akan a tabbatar da Adalci a kotun ƙolin Nigeria, wajen bawa al’ummar jihar Kano abinda suke muradi, domin yin hakan shi zai tabbatar da zaman lafiya da cigaba a jihar.

Yayin wani taro da Gamayyar ta gudanar a ranar Alhamis, Malaman sun bayyana adalci a matsayin abinda Allah yayi umarni akansa, koda kuma akan wanda ba’a so ne, da kuma bayyana illar zalunci da abinda yake haifarwa ga wanda yayi shi.

Malam Ali Dan Abba shi ne ya jagoranci taron, ya bayyana cewa, sun yaba kuma sun gamsu da kamun Ludayin gwamnatin Kano a cikin watanni shida, wannan ya basu ƙwarin gwiwar fitowa suyi kira domin samun adalci.

A yiwa Kano adalci ta hanyar tabbatar da abinda al'umma ke muradi - Gamayyar Malamai
A yiwa Kano adalci ta hanyar tabbatar da abinda al’umma ke muradi – Gamayyar Malamai

Wani labari : Ɗaya Daga Cikin Alƙalan Da Su Ka Samu Ƙarin Girma Jiya Ya Mutu Ana Kan Tuhumarsa Da Cin Hanci

Advertisment

 

Alƙalin Kotun Daukaka Ƙara da ke jerin waɗanda su ka samu ƙarin girma jiya ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin mai suna Shagbaor Ikyegh ya mutu ne a jiya Laraba 6 ga watan Disamba ya na da shekaru 65 a duniya.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da iyalansa su ka fitar a jiya Alhamis 7 ga watan Disamba a Makurdi babban birnin jihar Benue.

Sanarwar ta ce marigayin ya rasu ne a birnin Makurdi da ke jihar amma ba ta bayyana dalilin mutuwar tashi ba.

Ikyegh na daga cikin alƙalan da su ka samu ƙarin girma zuwa Kotun Ƙoli, kuma zai yi ritaya ne a shekarar 2028.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button