Dan Kwallo Ya sheƙa barzahu Ana tsaka da buga atisaye


Dan wasan kwallon kafa mai suna Sodiq Adebisi dan asalin Jihar Ogun ya rasu ana tsaka da atisaye a filin wasa na Dipo Dina da ke Ijebu-Ode.
Jaridar Leadership ta rawaito cewa dan wasan yana atisaye da wasu ‘yan wasan kwallon kafa a ranar Asabar lokacin da lamarin ya faru.


Lokacin da abokan wasansa suka ga matashin mai shekaru 34 a duniya ya fadi, sai suka garzaya da shi asibitin jihar da ke Ijebu-Ode.
Sai dai duk da irin kokarin da kwararrun asibitin suka yi, an tabbatar da rasuwarsa a ranar da aka kai shi asibitin.
Kakakin ‘yansandan jihar, Omolola Odutola, a ranar Talata ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayyana cewa, dan uwan marigayin, Ganiyu Adebisi, ya karbi gawar matashin don birne ta.
“Dan uwansa ya zo ne ya kai rahoton faruwar lamarin a sashenmu na Igbeba. Iyayensa sun ce ba sa son wani bincike kuma suna son a birne marigayin kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar, ”in ji Odutola.
Wani labarin: ‘Yan Sanda Sun Kama Barayin Motoci A Kano
Rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta ce ta kama mutane 15 tare da kwato motoci 20 da aka sace a sassan jihar.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Abdullahi Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Kano.
Ya mika godiyarsa ga jama’ar jihar kan hadin kai da goyon baya da ake ba su.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Usaini Gumel, ya jaddada aniyar rundunar na yin aiki cikin doka.
Ya kuma shawarci jama’ar jihar da suke kai rahoton duk wani mutum ko wani abu da ake zargi ga ofishin ‘yansanda mafi kusa domin daukar matakin tsaro cikin gaggawa.