Labarai

Abin da ya sa ministar Abuja take so a ‘dandaƙe masu fyaɗe’

Advertisment
Minista a ma’aikatar Birnin Tarayyar Najeriya, Ramatu Aliyu, ta ce tana so a rika dandake mutanen da aka samu da laifin fyade ne saboda hakan zai sa masu irin wannan ta’ada su ji tsoron yi wa mata fyade.
Ministar ta bayyana haka ne sakamakon kokawar da ‘yan kasar suke yi a baya bayan nan game da yawaitar matsalar fyade a kasar.
“Muna so a aiwatar da wata doka da za ta tabbatar da adalci. Daure wadanda aka kama da laifin fyade bai isa ba, don haka tabbas ya kamata a rika dandake su. Idan aka kashe su, ba za su tuna komai ba, amma idan aka dandake su za su ci gaba da rayuwa amma babu kuzari,” a cewar ministar.
Matsalar fyade dai tana neman zama ruwan dare a Najeriya, inda a baya bayan nan aka samun labarin yi wa wasu mata fyade a sassa daban-daban na kasar.
Daya daga cikinsu ita ce wata yarinya mai shekara 12 wacce ta shaida wa ‘yan sanda a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin kasar cewa wasu mutum 12 sun shafe wata biyu suna yi mata fyade.
Kazalika, a farkon wannan watan an zargi wasu mutane da kisan wata ɗaliba ƴar jami’a bayansun yi mata fyade a jihar Edo da ke kudancin Najeriya.
Masu rajin kare hakkin yara a Najeriya na ganin cewa za a ci gaba da fuskantar matsalar fyade ga kananan yara a kasar matukar gwamnati ba ta fara aiwatar da hukuncin kisa a kan masu aikata irin wannan laifi ba.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button