An bai wa Yusuf Buhari auren ‘yar sarkin Bichi a Kano


Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bai wa Yusuf Buhari, ɗan Shugaba Buhari na Najeriya, auren ‘yar Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero, ranar Lahadi.
Tawagar wakilai ta nema wa Yusuf auren Zarah Nasir Ado ne a hannun sarkin Kano, wanda yaya ne ga sarkin na Bichi.Kamar yadda bbchausa na ruwaito.
Wakilan da suka yi wa ɗan shugaban ƙasar walicci ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu ta ƙun shi haɗ da Gwamnan JIgawa Badaru Abubakar, da Ministan Shari’a Abubakar Malami.
Sauran su ne Gwamnan Borno Babagana Zulum, da tsohon Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari, da Mataimakin Gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna.
Daga bisani tawagar ta je garin Bichi domin gaishe da Sarki kuma surukin Shugaba Buhari wato Nasiru Ado Bayero.
Wata majiya ta shaida wa BBC Hausa cewa tambayar auren kawai suka je yi, wanda kuma Sarkin Kano Aminu Ado ya ba su, saɓanin rahotannin da ke cewa ɗaura auren aka yi.
Wasu majiyoyi sun ce matasan biyu sun haɗu da juna ne a Ingila yayin da suke karatu a can.
Yusuf ne ɗan Aisha Buhari na uku da zai yi aure tun da Muhammadu Buhari ya zama shugaban ƙasa a shekarar 2015.