Abdul Amart ya Bayyana Dalilin Sayawa Iyalan Marigayi Aminu S. Bono Gida


Fitaccen maishirya fina finan Hausa Abdul Amat Mai Kwashewa ya sayawa iyalan Marigayi Aminu S. Bono gida na sama da naira miliyan uku.
Da yake zantawa da Kanawa Radio jim kadan bayan kammala addu’o’i na musamman da kungiyar masu Bada umarni ta shirya a yammacin ranar Litinin a birnin Kano.
Mai kwashewa yace Aminu S. Bono na daga cikin mutanen da suka taimaka wajan kawo cigaba a kamfaninsa, saboda haka duk abinda yayiwa iyalinsa bai fadi ba.
A cewar sa, “Aminu S. Bono ya na daga cikin wadanda su ka taimakawa kamfani na na ABNUR Entertainment ya kai matakin da ya ke a yanzu”.
Ya kuke ganin irin wadannan abubuwan arziki da ‘yan Kannywood din keyiwa iyalan Marigayin.
A yau da munka zo sadakan bakwai nake ake cewa kamar wannan watan kuɗin hayar gidansa zai karewa sai nace to dan Allah a nemo gida kusa ga iyayensa kuma alhamdullahi anka samu duk da ban shirya hakan ba amma kuma an saye, babban abinda munka tattauna da yan uwana shine ta yadda zamu samarwa da iyalana jari babba da zasu iya cigaba da kasuwanci saboda halin yau da kullum.
Nagudu tv sun samu tattaunawa da Abdul amart mai kashewa tun daga can wajen sadakan bakwai inda bayyana dalilan sa.