Labarai

KUYI HAKURI: Nasara ga Azzalumi na karamin lokaci ne kawai kamar dai yadda Allah ya bawa Fir’aauna dama – Sanusi Lamido

Tsohon sarkin kano Muhammadu Sanusi Lamido Na II a wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumintar zamani an hango shi Yana cewa Idan kana tare da Allah karka ji Tsoron wanda yace shi ba Ruwansa da Allah domin ko da yayi wata Nasara ko galaba ta dan lokaci ne Dan Kadan, kuyi hakuri za ku ga karshen al’amarin yadda zai kare watakila Allah ya bashi dama ne domin ya halaka shi, ku duba fir’auna babu Abinda Baiyi ba kafin zuwan Annabi Musa da bayan zuwansa amma Annabi Musa yace kuyi hakuri Ubangiji zai halaka makiyinku Kuma haka Allah ya yi daga karshe.

KUYI HAKURI: Nasara ga Azzalumi na karamin lokaci ne kawai kamar dai yadda Allah ya bawa Fir'aauna dama - Sanusi Lamido
KUYI HAKURI: Nasara ga Azzalumi na karamin lokaci ne kawai kamar dai yadda Allah ya bawa Fir’aauna dama – Sanusi Lamido

Jama’a da dama na cewa wannan furuci na Muhammadu Sanusi Lamido na da nasaba ne da dambarwar Yanke hukuncin shari’ar jihar Kano.

Wani labarin : Shari’ar Zaben Gwamnan jihar Kano Kotun daukaka Kara na Shirin sauya ra’ayin jama’a Zuwa ra’ayin Siyasa – Jega

 

Tsohon Shugaban Hukumar Zabe INEC Farfesa Attahiru Jega Yace Kuskuren Kotun Daukaka Kara A kam Zaben Gwamnan Jihar Kano Abin Takai ne Ana Bukatar A Yi Cikakken Bincike.

Farfesa Jega jiya a lokacin da yake fira da gidan Television na Channel
ya yi Allah-wadai da hukuncin kotun daukaka kara ta jihar Kano, ya kuma zargi bangaren shari’a da yunkurin sauya ra’ayin jama’a domin ra’ayin Siyasa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA