Nadama ce 95 cikin 100 a zuciyar Buhari, ya kamata ya soma neman gafarar yan Najeriya – Rarara
A cikin wani bangare jawabin mawakin buhari dauda kahutu rarara yake cewa yanzu babu abinda a cikin zuciyar buhari sai na dama wanda tabbas ya kamata ya fara neman gafara yan Nigeria wandanda basu mutu ba.
Ga abinda mawakin rarara yake fadi akan Muhammadu Buhari
“Nadama ce 95 cikin 100 a zuciyar Buhari, ya kamata ya soma neman gafarar yan Najeriya wandada basu mutum ba, wanda suka mutu kuma su hadu a can.
Mutumin da daga karshe yazo yace a canza kuɗi duk mai mai naira dubu biyu sai da ya karye, duk wani mai dubu ɗari sai da ya karye , duk wani mai miliyan ɗaya sai ya karye, hukuncin duk mai mutum ɗari akwan mutum miliyan dari ankayi akwai hankali a cikin Wannan .
Tun kafin lokacin buhari ya hau mulki ina da arzikina daidai gwargwado rufin asirina inda wakar ma sai naga dama nakeyi.
Inda dan hakan ba za’a yimin tayin miliyan dari biyar ba 500million ince zanyi buhari ba, buharin na musulumu ne-inji rarara.
Daman nace ina jiran wandanda zasuyi magana akan maganganuna da nayi su bani amsa cewa na samu wani abu a lokacin buhari ko anyimin wani mukami to sai naga wandada sunkayi magana basu isa na basu amsa ba.
Domin su basusan ina anka je anka tashi ba har anka samu mulki ba, basu san ta yadda anka kama zomo ba har an ka zamo wani abu.
Amma shi wanda yake fadin cewa yayi wani abu an bashi mukami yazo ya fadi abinda yayi na bashi muƙamin gwamtani buhari ko ya samu kuɗi balantana rarara , ko shugaban kasa buhari bai kai ni bashi gudunmawa ba ya zamo shugaban kasa ko shi bai bayar da ita ba – inji rarara.
Rarara ya kara da cewa mutum daya ne yafini bada gudunmawa shine tinubu shi kadai ne mutum daya shi kadai ne kacal yafini baiwa buhari gudumuwa ya zamo shugaban kasa -inji rarara.
Ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da Freedom Radio bayan wancan jawabin da yayi.
Ga sautin hirar nan ku saurara kuji.