Labarai

Jami’ar FUDMA Ta Hana Dalibai Maza Da Mata Kama Gida Tare

Jami’ar Gwamnatin tarayya ta Garin Dutsinma dake Jihar Katsina FUDMA, ta haramta wa Ɗalibai Maza da Mata Zama a Gida guda, tare da bayyana wasu Unguwanni da ba’a yadda Ɗalibai su kama Gida a Wuraren ba.

Wata Sanarwa da ta fito daga Ofishin Shugaban Sashen kula da harkokin Ɗalibai na Jami’ar ta bayyana cewar, daga yanzu an haramta wa Ɗalibai Maza da Mata zama a Sansani guda, don haka duk wanda aka samu da hannu wurin aikata hakan zai Fuskanci Hukunci Kora daga Jami’ar.

Jami'ar FUDMA Ta Hana Dalibai Maza Da Mata Kama Gida Tare
Jami’ar FUDMA Ta Hana Dalibai Maza Da Mata Kama Gida Tare

Katsina post na ruwai haka kum, Sanarwar ta bayyana wasu Unguwanni da aka Haramta wa Ɗaliban dake zaune a Wajen Jami’ar zama da suka haɗa da, Unguwannin dake yankin Makarantar Maryamo Ajeri, da Unguwannin dake Saman hanyar Garin Tsaskiya, da kuma bayan Makabarta.

Sauran Unguwannin da aka haramta wa Ɗaliban Zama sun haɗa da, Bayan

Gidan Radiyo, da bayan Sansanin Jami’ar, da Wuraren da ke da alaƙa da Garin Dabawa, da kuma yankin Dangaje.
Sauran sun haɗa da, yankin dake kusa da Khadijah Bread, da kuma Unguwannin Lokwas dake bayan Makabartar Mustapha Nuhu Kuki dama duk wasu wurare da kan iya zama Barazana dake ciki da Sassan Garin na Dutsinma.

Kazalika, Sanarwar ta yi Gargaɗin Cewar, duk wani Dalibi da aka samu da saida Wurin Zama ko kuma wani ɓangare na Ɗakin kwanan sa da Jami’ar ta Mallaka masa, ga wani Dalibi ko kuma Ma’aikaci hakan zai iya kaishi ga fuskantar hukuncin Kora daga Jami’ar.

Daga karshe ta yi kira ga Dalibai su riƙa yin shiga wadda ta dace, tare da kauracewa Fita bayan karfe 10 na dare, da kuma sanar da duk wani abu da basu Fahimta ba zuwa ga Jami’an Makarantar domin Ɗaukar Matakan da suka kamata.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button