Kannywood

Musa mai sana’a ya bayyana mai gidansa a kannywood

Musa mai sana’a shiyasa ya samu hallarta Gabon talk show room inda ankayi masa tambayoyi sosai a cikin wannan shiri.

Musa mai sana’a fitaccen jarumin kannywood kuma mai daukar nauyi a harka kannywood inda yayi suna sosai a masana’atar kannywood, a shafin tiktok mai suna Momee Gombe real sune sunka wallafa bidiyon.

Musa mai sana'a ya bayyana mai gidansa a kannywood
Musa mai sana’a ya bayyana mai gidansa a kannywood Hoto/Instagram: musa mai sana’a

Musa mai sana’a ya nuna cewa shi asalin dan gwagwarmaya ne tun kafin yazo Masana’atar Kannywood, anyi masa tambaya wadda kowa yana son sanin amsar daga bakinsa.

Waye mai gidanka a kannywood?

“To gaskiya da akwai badan komai nace Miki da akwai ba, saboda kina ganin wasu nacewa basu da mai gida to duk labari ne, dirowa kayi kawai, to irin wannan ne ke sa wasu sukai ga Chi wasu su ki kaiwa.

Duk butulci ne kuma duk butula baya zuwa ko ina a duniya kuma baya nasara, duk wanda ya kyautata maka kasan ya kyautata maka, duk wanda yayi maka rana kasan yayi maka rana, kuma duk wanda ya girmeka kasan ya girme ka, ka girmama na gaba da kai sai kaga abu yayi albarka.

Musa mai sana’a ya kara da cewa:

“Ko ilimi ne sai kaga wasu sunje sunyi karatu baida rana suna watangaririya wajen neman aiki ka rasa. sai kaga mutum Ance anyi digiri ko diploma amma sai kaga mai saida rake ma yafika natsuwa.kesan dalilin haka shi wanda ya koyama karatun ya kunkayi da shi ka girmama shi balantana ka samu albarka wannan karatu.

To ni idana da mai gida wani bawan Allah wanda ake cewa salisu you men shine mai gidana kuma har gobe duk inda naje ina nuna shine mai gidana kuma ina girmama shi, domin in ance wannan mai gidansu ne bazasu fada ba, saboda suna ganin ae lokacin sune ko zamanin su ne ko sun samu wani abu wanda yafi na wancan.

Ko mai na zama shine mai gidana.” – inji Musa mai sana’a

Zaku iya kallon bidiyon a Nan







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button