Mansurah Isah ta fashe da kuka saboda tausayin yaron da mahaifinsa ke zargin Aljani ne


KWANAN baya a soshiyal midiya wata mata ta wallafa hoton wani yaro mai suna Halifa mai fama da wata cuta, inda ta riƙa zagin halittar sa, ta na tambayar sa shi mutum ne ko a’a.
A bidiyon, an ji yadda yaron ya na ce mata shi mutum ne, amma ta dage sai ya bar mata gida a dole domin wai ta gaji da ciyar da shi amma ga shi nan ko da yaushe a bushe.
Bidiyon ya ɗauki hankali a soshiyal midiya inda jama’a su ka tausaya wa yaron, tare da neman inda ya ke.
A wani bidiyo da tsohuwar jarumar Kannywood Mansurah Isah ta saki cikin takaici a shafin ta na TikTok, ta nemi duk wanda ya san inda matar ta ke ya faɗa mata za ta ba shi N50,000, idan kuma ya bayar har da lambar wayar ta za ta ba shi N70,000.
A binciken da wani mai rajin taimakon marasa ƙarfi a TikTok, Aminu J. Town, ya gudanar ya bayyana cewa sun gano matar kuma an damƙa ta ga hannun hukuma.
cewar sa, tuni yaron ya fara karɓar magani.
A lokacin da Mansurah Isah ta je gidan su yaron don tallafa masa tare da ci gaba da kula da lafiyar sa ta fashe da kuka ganin irin halin da ta same shi a ciki.
Mansurah ta yi alƙawarin tallafa wa yaron don ganin rayuwar sa ta inganta bayan nema masa lafiya da za ta ci gaba da yi.
Wannan mutumim da kuke gani, shine real Hero a rayuwar Khalifa.
Lokacin da kowa ya guje shi, uwar ma ta tafi ta bar shi, matar shi ta nemi saki ta rabu dashi ( kakar Khalifa) shine cin Khalifa, shan Khalifa, wanka, wanke kashi da sauran su na Khalifa.
Yana tura kuran ruwa dan ya ciyar dashi.
Kuka yake tayi. Yace Khalifa ina son ka samu kulawa da lafia shi yasa zan barka ka tafi, in ba haka ba, da inada hali da lafia, da bazan barka ka tafi ba.
Baba, In shaa Allah bazakayi danasani ba. Allah ya bawa @laylahaliothman ikon Kyla dashi ameen.
Yaro dai yana samun kulawa ta musamman gashi nan wajen shakatawa tare da Mansurah Isa.