Labarai
An koma makarantu a yankunan da girgizar kasa ta afku a Maroko
Advertisment
Yara sun koma makaranta a garuruwa da ƙauyuka da dama a Moroko bayan mummunar girgizar kasar da ta afku a kasar, kamar yadda kafafen yada labarai suka rawaito.
BBC Hausa na ruwaito.A wurare kamar Amizmiz da Asni da Taroudant, an ci gaba da ɗaukan darussa tare a cikin tantuna 150 waɗanda aka samu tallafi daga hukumomin yankin na musamman da aka tanadar don koyarwa, a cewar shafin intanet na Lakome mai zaman kansa.
Kamfanin dillancin labaran kasar MAP ya bayar da rahoton kyakkyawan fata da jajircewa a tsakanin malaman da daliban.
Bugu da kari, ana jigilar dalibai 6,000 daga yankunan da lamarin ya shafa a El Haouz zuwa makarantu a birnin Marrakesh, kamar yadda gidan talabijin na 2M ya ruwaito.