Labarai

Kotu ta daure mutumin da ya saci lemon kwalba a Adamawa

Wata kotu a jihar Adamawa ta yanke hukuncin daurin watanni 6 ga wani matashi Nafi’u Sabe da aka samu da laifin satar katan 6 na maltina.

An dai yanke masa wannan hukunci bayan da ya amsa laifinsa na satar wannan maltina.

Jaridar Dclhausa na ruwaito alkaliyar kotun Hafsat Abdurrahman ce ta yanke wannan hukunci.

Nafi’u Sabe ya amsa laifinsa inda ya ce ya saci wannan maltina ne a kasuwar Jimeta jihar Adamawa a Agustan, 2023, inda ya yi nadamar aikata hakan.

A wani labari na daban : Nijeriya ta biya bashin Naira tiriliyan 2.34 cikin watanni 6 – DMO

Hukumar kula da basukan Nijeriya ta DMO ta sanar cewa kasar ta kashe kudi Naira tiriliyan 2.34 wajen biyan basuka a cikin watanni 6.

A rubu’i na biyu na shekarar 2023 dai, kasar ta biya bashin Naira bilyan 849.58. Bayanai daga hukumar ta DMO sun ce a rubu’in farko na shekarar ta 2023 an biya bashin Naira bilyan 874.13 na cikin gida tare da bilyan bashin kasashen waje na Naira bilyan 617.35.

DMO ta ce jimilla kudin sun kama Naira tiriliyan 1.24.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button