Labarai

Duk alƙalin da ya juya zaben kano ya shiri haddasa bala’i da tarwatsa kano – cewar Kwamishina Adamu Aliyu

Advertisment

Kwamishinan Kasa da Sufiyo na jihar Kano, Adamu Aliyu ya gargaɗi Alkalan da za su yanke shari’ar zaɓen gwamnan Kano cewa duk wanda ya karɓi cin hanci ya juya shari’ar gwamnan Kano, zai ga ‘Bala’i’.

Ya faɗi haka a bidiyo da aka saka a shafukan sada zumunta wanda shi da kansa ya tabbatar da wannan sako da ke cikin bidiyon.

Jaridar Premium Times Hausa na ruwaito kwamishina Aliyu ya bayyana cewa akwai raɗeraɗin cewa akwai waɗanda ke yi wa Alkalan tayi cin hanci har naira biliyan 10 domin a kwace gwamnatin Abba a baiwa APC da jam’iyyar ta kada a zaɓen gwamman jihar na 2023.

” Abinda na ke so in gaya wa duk waɗanda ke kokarin yi wa Shari’ar zaɓen gwamna katsalandan cewa ya kwana da shirin ganin bala’in da bai taba ganin irin sa. Ita kanta jihar Kano za ta tarwatse, don ba za mu yarda ayi mana karfakarfa ba.

” Ina gargadin alkalan kotun su sani, duk alkali da ya bari a yi amfani da shi ya karbi cin hanci ya yanke hukuncin da ba haka ba, muna so mu gaya masa ya zabi tsakanin ransa da kudin cin hancin da ya karba.

” Kuma ina so ku gani kuma ku sani, bala’in kashe-kashen da ƴan Kaduna, Katsinawa da Zamfara suka yi fama da shi, zai zama wasan yara, domin na Kano sai ya dama haka ya shanye, idan aka kwace kujerar gwamnan Kano.

Kwamishina Aliyu ya tabbatar mana da cewa ya faɗi haka kuma bai janye koda harafi daya saga cikin kalaman sa ba.

Har yanzu dai ana jiran kotun sauraron kararrakin zaɓen gwamna, ta yanke Shari’ar Zaɓen gwamnan Kano da na wasu jihohin da ake kalubalantar sakamakon zaɓukan

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button