Labarai
An Daura Auran Muhammad Mai Shekaru 18 Da Amaryashi Sumayya ‘Yar Shekara 16 A Tilden Fulani Dake Jihar Bauchi (hotuna)
Advertisment
A yau Jumma’a a garin Tilden Fulani karamar hukumar Toro dake jihar Bauchi, aka daura Auran Muhammad Ahmad Salihu, mai shekaru 18 da amaryarshi Sumayyah Adam Ibrahim mai shekaru 16,kamar yadda shafin Facebook mai suna Daily News Hausa na ruwaito
An daura Auran ne a babban masallacin Izala dake garin Tilden Fulani. An gudanar da shagulgulan
bikin su cikin farin ciki da annashuwa.
Ango Muhammad Ahmad Salihu, mazaunin anguwan Nasarawa Jahun dake cikin kwaryar jiharBauchi, Amaryar kuma ‘yar Tilden Fulani ce.
Muna musu Addu’ar Allah ya bada zaman lafiya da zuri’ah dayyi ba. Amin










Allah ya basu zaman lafiya