Labarai

Maganar shan jini Gaskiya ne : Daga amsa sallama sai ta yake jiki ta fadi sai amai – Cewar Jamila Ibrahim

A yan kwanankin bayya anyi zargin mata masu zuwa gida suyi sallama sai su shanye jinin mutum wanda labarin yayi matuƙar yade kafafafen sada zumunta shine yau wata yar uwa mai amfani da kafafen sada Jamila Ibrahim ta wallafa wani labari mai ban tsoro akan yadda wannan abun ya faru a unguwar su.

Ga abinda ta wallafa a shafin ta na sada zumunta.

Nesa yau yazo kusa , abinda mukeji yana faruwa wani wajan yazo har cikin unguwar mu kuma ya faru da makociyar mu , daga amsa sallama da gaisuwa nan take ta fadi tanata amai numfashinta sai hawa yake yaki sauka kuma amai yaki dainawa …

Cikin hukuncin Allah akwai waenda sukaga faruwar abin aka rike matar aka kaita wajan mai ungwa tanata confessing wai sunada yawa masu irin wannan abun , da kyar aka mata ta sake mata numfashin ta ya fara dawowa , haryanzu da nake wannan rubutun neighbor Dina a galabaice take …

An dai kira yan sanda Suzo su shida abin kuma a kara bincikan abinda ke faruwa …

Jama’a idanma kuna ganin kaman karya ake kuzo in kaiku har wajan mai ungwa ku gani wa idonku ko kuji da kunnuwan ku …

Don Allah mu kula ba karya bane , yau munga zahiri ..

Kar kuga bakon mutum ku tsaya magana dashi ,mu cigaba da addu’a Allah ya tsare mu baki daya.”

hausaloaded mun tattaro kadan daga cikin martanin mutane wanda sunka tofa albarkacin bakinsu akan wannan rubutun.

 

@Ibrahim sheikh Adam  cewa yake :

Wallahi nima ya faru da wata yarinya Makwafciyata. 

Amma har yanzu wasu cewa suke wai karya ne.

@Umar Abusufyan yusuf cewa yake :

Malaria, typhoid ce hade da yunwa, sai ace mayu ne.

@Muazu Abu Juwairiyya hadeja cewa yake :

Idan mutum yana da labari cewa hakan na faruwa, to daga anyi sallama idan ya tsorata sai ku dauka hakan ce ta faru.

So wani lokacin mutane ne suke kaduwa saboda kururuwar da akayi.

@Isah Jibrin cewa yake :

Wannan lamari akwai daure kai ALLAH ya kyauta. Toh amma nidai awannan lamari baniyadda saina gani zahiri kam.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button