google-site-verification=WmtThtgKMuimwQoXo8Cd4z9ZhII1jY-1XVfjGSvL5r8
Labarai

Abin a yaba : Rarara ya bada aikin Tituna bakwai 7 a jihar katsina

Yanzu nan majiyarmu ta samu wani labari wanda tabbas abin a yaba ne irin yadda shahararren mawakin siyasa Dauda kahutu Rarara yayiwa mutanen jiharsa albishir mai mai dadi.

Majiyarmu ta samu wannan labarin daga mai taimaka masa na musamman Rabiu garba gaya inda yake sanar da al’ummar cewa mai gidan ya bada kwangilar tituna guda bakwai a mahaifinsa ga yadda sanarwa ta kasance.

Mai Girma Shugaban Kasar Mawaka Alhaji Dauda Kahutu Rarara, Ya Bada Aikin Titin Tudun Wakili Zuwa Sundu Zuwa Danja Zuwa Garin Dabai, Aikin Titin Zai Wuce Zuwa Garin Kahutu Daga Kahutu Zai Wuce Zuwa Garin Chediya, Daga Garin Chediya Kwaltar Zata Wuce Har Zarewa.

Jama’ar Wannan Yankin Suna Godiya Tare Da Fatan Allah Ya Rabaka Da Hajiya Lafiya.”

Tabbas wannan abin a yaba ne domin irin yadda yake kyautatawa al’ummarsa musamman irin yadda muke kawo muku labarai na irin yadda yake rabawa al’ummar kahutu alkhairi na abinci da kuɗin cefane.

Ga hotunan inda ake aiki nan.

Abin a yaba : Rarara ya bada aikin Tituna bakwai 7 a jihar katsina Abin a yaba : Rarara ya bada aikin Tituna bakwai 7 a jihar katsina Abin a yaba : Rarara ya bada aikin Tituna bakwai 7 a jihar katsina

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button