Labarai

Siyasar ubangida ce babbar illar mulkin farar hula a Najeriya – Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayyana siyasar ubangida da babbar illar mulkin dimokraɗiyya a tsawon shekaru 25 a Najeriya

Attahiru Bafarawa ya shaida wa BBC hakan ne a wata hira da ya yi dangane da cikar mulkin dimokraɗiyya 25 ba tare da katsewa ba.

” Mu da muka zo ba mu da ‘kingmaker’ wato ubangida, kowane gwamna zaman kansa yake amma bayanmu sai aka mayar da abin ubangida. Wasu gwamnoni ba su da kuɗin takara sai wasu su ba su saboda haka idan suka samu kujerar dole ne su biya. Wannan ya sa siyasa ta lalace saboda ta zama kamar zuba jari.”
Á
Wani ƙalubalen da tsohon gwamnan ya ce shi ma ya yi wa dimokraɗiyya dabaibayi, shi ne yadda aka talauta ‘yan Najeriya amma idan lokacin zaɓe ya yi sai a fito musu da kuɗi.

“Hakan ya janyo jama’a sun zama mayunwata.” In ji Bafarawa.

Dangane da irin cigaban da aka samu a mulkin dimokraɗiyya, Bafarawa ya lissafa abubuwa kamar kwanciyar hankali da Ilimi da noma da zaman lafiya da kuma ƙaruwar arziki.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button