Labarai

Bidiyon Badakalar Kudi Naira Tiri’iyan 89 da Hon Gudaji Kazaure Ya fasa kawai

Najeriya Na Da Hannu Kan Badakkalar Naira Tiriliyan 89 -Hon Gudaji Kazaure

A Najeriya, wani kwamiti na musamman da shugaban kasar ya kafa domin ya gudunar da bincike a kan cajin cirewa da ajiyar kudi a asusun banki ya yi zargin cewa wasu hukumomin da binciken ya shafa suna kokarin hana shi yin aikin sa, da kuma hana shi ya mika wa shugaba Buhari rahotonsa.

Kwamitin wanda aka dora masa alhakin binciken cajin kudin ajiya da cire kudin tun daga shekara ta 2013 zuwa yanzu ya gano cewa babban bankin kasar ya tara fiye da naira tiriliyon tamanin, amma ya yi zargin cewa ana sama da fadi da kudin.

Muhammad Gudaji Kazaure, shi ne sakataren kwamitin kuma ya shaida wa BBC cewa kwamitin shugaban kasar ya gano wasu makudan kudade:

Bidiyon Badakalar Kudi Naira Tiri'iyan 89 da Hon Gudaji Kazaure Ya fasa kawai
Najeriya Na Da Hannu Kan Badakkalar Naira Tiriliyan 89 -Hon Gudaji Kazaure

“Kwamitinmu ya gano naira tiriliyan 3.9, kuma yayi kokarin shiga babban bankin Najeriya domin gano inda wadannan kudaden suke cikin asusun ajiya guda uku.”

Ya ce akwai naira biliyan 171 na cikin asususn ajiya na farko zuwa shekarar 2020, kuma akwai bashin naira tiriliyan 23.4 da aka ba bankuna, kuma akwai bashi da ake ranta wa gwamnati na tiriliyan 13.

“Ta ina aka samu wadannan kudaden. Kudin gwamnati ne ake ranta wa gwamnati?”

Ya tuhumi cewa kudaden da bankunan Najeriya naira dari-dari ne aka tara har aka sami wadannan tiriliyoyin kudaden na shekaru hudu zuwa shida.

“Kudi ne da ba a sakawa cikin asusun ajiyar gwamnati – daga asusun ajiya mallakin wasu mutane ake tura su asusun masu zuba jari (investors account), shi ke nan sun zama mallakinsu,” inji shi.

Gudaji Kazaure ya kuma ce ana yi musu nuku-nuku kan binciken da shugaban kasa ya bukaci su yi.

“Shi gwamnan babban banki da alkalin alkalai hankulansu sun tashi da na fara wannan bincike, haka ma ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnati.”

Ya tuhumi ministan shari’ar da “yakar kwamitin domin ya rubuta wata wasika” domin dakatar da aikin kwamitin.

Ya kuma ce wasu mukarraban shugaban kasa suna hana shi ganinsa domin sanar da shi halin da ake ciki kan wannan binciken.

“Shugaban kasa ya ce duk mako na rika zuwa wajensa domin sanar da shi halin da ake ciki, sai dai bayan wata guda na fari na bukaci ganin shugaban kasa amma jami’insa na ‘protocol’ ya ce ba zan ga shugaban kasa ba.”

Ya kara da cewa shugaban kasar ya umarci kwamitin da ka da yayi aiki da kowa, “domin dukkansu su na nan wannan badakala ta faru ba su yi komai a kai ba, face shugaban hukumar tsaro ta farin kaya, DSS.”

Ya tuhumi gwamnan babban banki da “wadanda suka saka shi a wurin”, da wasu da yake ba daloli a farashin gwamnati domin su sayar su ci riba, da kuma wasu da yace ke amfanar gwamnatin – cikin wadanda suke amfana da badakkalar.

Ya bayyana fatansa kan aiki kwamitin kamar haka:

“Gwiwa ta ba ta yi sanyi ba, hasali ma ina jiran lokacin da shugaban kasa zai umarce ni da in kama gwamnan babban bankin Najeriya in kulle, tare da wasu jami’an gwamantinsa da ke ma sa zagon kasa, su ma duka in cire su in bincike su.”

Haka kuma ya ce lallai akwai wannan kudi naira tiriliyan 89, kuma “suna iya biyan bashin da ake bin Najeriya kaf!” Kuma tilas a cire gwamnan babban bankin Najeriya domin ya ce, “idan yana kan mukaminsa, ba zai bari mu gudanar da aikinmu na binciken central bank ba. Ba zai bari ba

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button