Labarai

Saurayi yayi kokarin yankewa mahaifiyarsa farji saboda tana zina a bakin titi

Advertisment

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta damke wani mutum mai suna Joshua Adetutu mai shekaru 22 bayan da yayi yunkurin yanke gaban mahaifiyar shi saboda zargin ta da yake da bin maza

Kamar yadda Gistmania ta ruwaito, lamarin ya faru ne a titin Odobanjo kusa da titin Gwamna da ke yankin Ikotun a jihar Legas inda mahaifiyar matashin ke zama da mahafiyarta. An gano cewa Joshua ya garkame mahaifiyar shi a daki ne tare da dauko wuka don aiwatar da nufin shi. Jaridar legit na ruwaito.

Saurayi yayi kokarin yankewa mahafarjin mahaifiyarsa saboda tana zina a bakin titi
Saurayi yayi kokarin yankewa maha farjin mahaifiyarsa saboda tana zina a bakin titi Hoto/Google

Ya tureta kasa ne tare da yunkurin yanke gabanta. Amma kuma Jennet ta samu taimakon makwabtansu wadanda suka cece ta tare da kiran ‘yan sandan yankin Idimu da ke Legas

An kama Joshua tare da garkame shi. A yayin da ‘yan sanda ke tambayar shi, Joshua ya zargi mahaifiyar shi da tozarta shi tare da bashi kunya kuma bata mutunta kanta a yankin.

Advertisment

Jennet ta yi aure ne inda ta haifa Joshua da sauran ‘ya’yanta kafin ta rabu da mahaifinsu don rayuwa ita kadai. Da farko dai Joshua na zama da mahaifinshi amma sai ya damfareshi kuma yayi zaman gidan yari na Badagry. Jennet ce ta dinga fafutukar fito da Joshua kuma ya fara rayuwa tare da ita a wajen mahaifiyarta.

A nan ne ya gane cewa mahaifiyar shi na yawan samun baki maza wadanda ya zarga da lalata da ita. Don haka ne ya yanke hukuncin yanke gaban ta baki daya, lamarin da ya kai shi hannun ‘yan sanda.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button