Talauci : Labarin wani dalibin Jami’a dan aji 3 mai ban tausai da imani
A yau din nan mun hadu da wani labarin yanayin wani dalibi wanda tabbas akwai tausayi da darasi duba da irin yanayin da ya shiga rashi da sai ka zubda hawaye barr. Abba shuaibu Gidan wanki ne ya wallafa labarin a shafinsa na sada zumunta.
Dazu wani dalibin jamia ya same ni ya ce yana so nataimakeshi na hada shi da wanda zai ara masa kudin da zai biya kudin makaranta saboda yana aji na biyun karashe kuma zaa rufe. Yace don Allah ka taimaka kazama shaida idan ban biyashi ba ya dauki ko wane Irin mataki yaga ya dace!
Nace masa idan aka sami wanda zai ara maka, Taya zaka biyashi? Sai yace, “Allah zai isar min na biyashi” Na Kara tambayarsa, a Hostel yake ko zuwa da dawowa yake? Sai yace a Hostel, amma yanzu bazai iya biya ba zai koma jeka ka dawo. Naka Kara tambayarsa Idan ka koma jeka ka dawo, ya zakayi da kudin mota duba da tsadar mai, yace Idan wanda zan hada shi dashi zai bashi aro har kudin Hostel da zaifi. Na Kara tambayarsa, toh, ya zakayi da abinci Idan kana Hostel duba da tsadar rayuwa, yace “zan dogara da Allah”
Lamarinsa ya ta da min hankali ya kuma tuna min lokacin da nake Jamiar Bayero Kano, wanda da kyar da gumi nake hada 25k-30k. Wasu lokutan harda roko da yar murya. Yau gashi wani na neman 100k da wani abu!
Allhamdullah, bayan zubar masa da kawalla sai na tuntubi abokaina guda biyu, Namiji da Mace. Nagaya musu halin da ake ciki, nan take namijin yace “dole muhadu mu uku mu taimakeshi ko Allah yayi fushi damu.” Ita kuwa macen tace da yaran turanci, “let’s contribute 100k per head and assist this guy for the sake of Allah”.
Allhamdullah! Nan take muka hada 300k domin tallafa masa. Da na kirashi nace masa Ina son ganinsa, na kuma gaya masa cigaban da aka samu, yazo sai ya zube kasa yana kuka nayi ta rarrashinsa amma kuka yaki tsayawa! Ban san lokacin da na fara zubda kwallaba sai kawai ji nayi wata mata na cewa, “Barrister rashi akayi kuke kuka haka?”
Nan da nan na goge fuskata. Na bukaci ya bani account domin na tura masa 300k. Sai ya kauda Baki yace, “duka kudin nawa ne?” Nace e, ai duk naka ne. Sai yace akwai wata abokiyar karatunsa wadda har ta kwashe kayanta daga Hostel ta koma garinsu sakamakon iyayenta basu da halin biya mata kudin makaranta. “Idan zai yuyu a bata rabin kudin tunda duk hali daya muke ciki” Nan take ya kirata a waya yayi mata albishir. Ta fashe da murna. Yanzu haka zata dawo Kano gobe don ci gaba da karatunta itama.
Allah ka dubi dalibai talakawa.