Labarai

kawar Hadiza Gabon,Laila Uthman Tayi Goma Ta arziki

A yau shafinmu Hausaloaded ya samu wani labari wanda shahararriyar marubuci kuma shugaban charity foundation fauziyya D.suleiman na wallafa a shafinta na kafa sada zumunta.
 
Ga abinda ta wallafa.
“Ina zaune aka kira wayata, ina dagawa na ji muryar @laylahaliothman ta ce sunana Laila, na ce na gane ki ranki shi da dade, sai ta ce daman na kira ki ne domin na sanar da ke gidan abincimu na @landnkitchen ya ajiye gidauniyar taimako (Charity donation) domin bayar da taimako ga foundation din ku @creativehelpingneddyfoundation, mun ware kaso biyar na cinikinmu na duk wata za mu dinga baiwa gidauniyar domin taimakon mabukata.
Ta kara da cewa ga hoton box din da mu ka ajiye na wannan watan, amma za ki iya turo irin abun da ki ke bukatar a rubuta a box din sai mu cire wannan mu saka, sannan ki turo account za mu turo miki wanda mu ka tara na wannan watan.
Wallahi na yi matukat farin cikin da na jima ban yi ba, yanzu duk wata akwai kason foundation a @landnkitchen domin taimakawa mabukata, Allah ya sawa kasuwancinki albarka, Allah ya faranta miki duniya da lahira. Anty Hauwa da ki ka zamo tsani Allah ya biya miki bukatarki kema duniya da lahira. @hauwamustaphababura.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA