Kannywood

Jaruma Amal Umar ta Fadi Gaskiyar abinda yake tsakaninta da tsohon saurayinta

Fitacciyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Amal Umar, ta bayyana gaskiyar lamari kan zargin da wani tsohon saurayinta ke mata na cinye masa kudi.

Idan dai za ku tuna, jaruma Amal na fuskantar tuhuma na damfarar wani tsohon saurayinta kudi wanda yawansu ya kai kimanin Naira miliyan 40. Jaridar legithausa na ruwaito wannan labari.

Sai a wata hira da abokiyar sana’arta Hadiza Aliyu Gabon ta yi a shirinta mai suna ‘Gabon’s Room Talk Show’ jarumar ta ce sam zargin da ake yi mata ba gaskiya bane.

Maganar aure ta shiga tsakaninmu da shi

Jaruma Amal Umar ta Fadi Gaskiyar abinda yake tsakaninta da tsohon saurayinta
Jaruma Amal Umar ta Fadi Gaskiyar abinda yake tsakaninta da tsohon saurayinta Asalin Hot/ Amal Umar/Instagram

Hasalima ta ce sabanin abun da take fadi, ita ce ta kai tsohon saurayin nata kotu saboda girman zargin da yake mata.

Ta ce shakka babu saurayin ya yi mata alkhairi a lokacin da yake nemanta domin a cewarta har maganar aure ta shiga tsakaninsu domin iyaye sun shiga lamarin.

Sai dai ta ce da tafiya tayi tafiya, sai ta gane yana yi wa mata facakar kudi ta hanyar siya masu manyan motoci, gida, filaye a Kano lamarin da yasa suka rabu.

Amma kuma a lokacin da ya shiga matsala sai ta dunga tausaya masa.

A cewarta ya shiga harkar ‘crypto ne’ inda ta ritsa da shi lamarin da ya kai ga ita ce ta dunga taimaka masa da kudade.

Jarumar ta kuma ce abun ya kai har ta kusa siyar da motarta saboda ta taimake shi amma sai daga baya ta ji wai ana nemanta kan zargin sun aikata damfara tare.

Jarumar fin din ta ci gaba da cewar matashin na so ya huce takaicin kashewa yan mata kudi da ya yi ne amma sai ya zabi yin ramuwar gayya a kansa saboda ita yar fim ce.

Ta ce:

Kawai daga baya na ji wai ana nema na, me nayi? wai na ci kudi saboda ya san a cikin matan da ya yi mu’amala da su nice ya zo gidanmu ya yi magana da iyayena, ya san komai da komai nawa toh bari ya rama a kaina saboda kuma ina ganin ni yar fim ce, kin san kallon da ake yi wa yan fim daban da sauran matan da suke waje, yana ganin ai ni wurina za a samu kudi. Shine aka zo aka yi wannan abun amma abun da mutane suke tunani ba haka bane.

Kan inda magana ta tsaya, jarumar ta ce har yanzu magana na a gaban kotu kuma ance shi ya kai ni kotu, ba shi ya kai ni kotu ba saboda ana tuhumata da abun da ban san da shi ba kuma girman abun kamar ana so a lakaya cewa tare da shi muke yi da shi amma sai aka ce shi ya kai ni.”

Ga bidiyon nan domin kuji cikakken bayyani daga bakinta.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button