Kannywood

Harkar waka Ba’a samu Wani Ci Gaba Ba – Mahmoud Nagudu

Bayan tsahon lokaci ba tare da masoya sun ji muryar mawaki Mahmoud Nagudu ba, wanda ya kasan ce daya da ga fitattun mawakan da su ka shahara kamar shekaru goma da suka gabata, wanda a wancan lokacin ya yi shaharar da babu wani mawakin da ya sha gaban sa saboda daukakar da ya samu a wancan lokacin.
Northflix ta ruwaito.

Mawakin yana tabo bangare  daban daban a wakokin sa, kamarsu  soyayya, fadakarwa, da kuma yabon Manzon Allah S A W.

Sai dai lokaci mai tsawo ya shude ba a jin mawakin ko ganin sababbin wakokin sa. Wannan dalilin yasa da ya cikin wakilan mu ya bukaci ya ji ta bakinsa  dangane da rashin ganin wakokin na sa tsawon lokaci.

Tambayar farko da muka fara yi masa dangane da rashin ganin wakokin na sa ya fada mana cewa.

“Maganar gaskiya ina nan ba wani waje na je ba, sai dai, ni abin da na yarda da shi, shi ne, komai na duniya lokaci ne, domin haka shi mutum a kan sa ya kamata ya canza salo saboda tafiyar zamani.

Abin da na sani shi ne, na yi wakokin finafinai da dama, amma ban sa mu daukaka ba a wakar fim sai da na yi album Tattausan lafazi, domin haka ne ma daga wannan sai na canza wa kaina tsari. Domin hadisin Manzo ya na ce wa “Duk abin da ya yi kololuwa, to wata rana zai yi kasa”, Domin haka ne na canza wa kaina tsari. Wannan ta sa na gano yawan wakoki  ba su ba ne shaharar mawakin ba. kowa ya san  mawaki Michael Jackson, amma wakokin da ya yi, ba su kai rabin wakokin da na yi ba, don haka na gano yawan waka ba shi ba ne shahara”.

Mun kara tambayar shi, ko ya ya ke ganin harkokin waka a yanzu?

Sai ya ce “To ni a gani na waka ta na yin kwan gaba kwan baya ne, domin abin da mu ka yi a baya shi ne dai yanzu mu ke kara maimaitawa, haka masu kidan mu, domin haka muna nan ne dai a waje daya. ” Inji Mawaki Mahmoud Nagudu

Idan ma an ce an samu ci gaba, to bai wuce a ce yanzu an fi sauraron wakokin mu a duniya ba, amma dai ba ta bangaren inganci ba. “

Daga karshe ya yi kira ga mawaka da su ci gaba da harkokin ta hanyar tafiya da zamani kuma su hada kai. Sannan duk abin da mawaki zai yi, yana da kyau ya nemi ilimi domin kada ya yi abin cikin jahilci saboda inganta sana’ar waka.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button