Kannywood

Ko Kusan Dalilin Da Yasa Maryam Yahaya Ta Cire Hudar Hancinta ?

A kwanakin baya ne aka samu bambancin ra’ayin mutane da ya janyo ce-ce-ku-ce sakamakon wani sabon salo da matashiyar jaruma Maryam Yahaya ta fito da shi na huda hanci tare da Makala wasu karafuna masu  kama da asirka.

Duk da kasancewar lamarin ya zama sabo a wurin mafi yawan masu bibiyar Kannywood, amma ba jarumar ce ta farko da ta fara yin wannan hudar hancin ba, domin kuwa kafin ita sananniyar fuska kuma kawa ga jarumar wato Najla Muhammad wacce aka fi sani da Murjanatu ‘Yar Baba ita ta fara yin wannan hudar hancin, sai dai ita nata bai yi zafi kamar na Maryam Yahaya ba.

Jarumar ta hadu da fushin masoyanta ne lokacin da ta sanya hotonta mai hudar hanci a shafinta na Instagram, inda mutane suka rika tofa albarkacin bakinsu.

Adamu Hassan Ali, wanda daya ne daga cikin wadanda suke bin jarumar a shafinta na Instagram din cewa ya yi: “Gaskiya ki cire wannan dan kunnen, domin bai yi miki kyau ba, bai kuma dace da ‘yar musulmi ba.”

Yahaya Usman cewa ya yi “Plz ur beautiful and best actress of kannywood, why do you choose to spoil ur image, remove the ring from ur nose is not important and it doesn’t match you,” (don Allah kina da kyau kuma babbar jaruma a kannywood, me ya sa za ki zabi bata sunanki, ki cire wannan abin daga hancinki ba shi da amfani kuma bai dace dake ba a matsayinki na musulma).

“Kai ikon Allah wallahi ni ma na gano abin hancin kwata-kwata bai yi mata kyau ba, amma ba na son na yi magana ne saboda kar ki ji abin babu dadi, kin fi kyau babu shi gaskiya,” in ji Safeetadoul.

Sai dai masu iya magana kan ce daidain wani karkataccen wani, domin masoya jarumar murna da farin ciki suka nuna, kamar yadda Zainab Abdullahi Pretty ta ce, “Kin yi kyau sosai. Abin hancin kuma ya burge ni.

Ita ma Ummi Kano CTY ta ce, “Don Allah ina son wannan hujin hancin.”

Bayan wannan musayar yawon ne kuma sai kuma ga jarumar ta sanya wani hoto ba tare da hujin hancin ba, abinda ya sa ake ganin jarumar ta cire ne saboda masoyanta da suka nuna basa so.

Ahmad sarauniya: “Gaskiya Maryam na ji dadin daukar shawarar masoyanki da kika yi na cire wannan abin na hancinki wallahi, Allah ya kara daukaka.”

Mun yi kokarin ganawa da jarumar saboda jin ainihin dalilin nata sai dai hakan bai samu ba sakamakon rashin samunta a waya da aka yi.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button