Kannywood

Ahmed Musa ya cika Alkawari, ya siya Wa Baba Karkuzu Gida Da Kyautar 500K (cikin hotuna)

A yanzu nan majiyarmu ta samu labarin alkawalin da yayi wa tsohon jarumi da lalura ta same shi inda yanzu nan mun samu labarin daga shafin zinariya tv cewa an sayawa baba karkazu gida da kuɗin a hannunsa.

Ahmed Musa   ya cika Alkawari, ya siya Wa Baba Karkuzu Gida Da Kyautar 500K (cikin hotuna)
Wannan shine gidan da anka sayawa baba karkazu

Mai rike da kambun Super Eagles Ahmed Musa ya cika alkawarin da yayi na siyawa Mallam Abdullahi Shu’aibu wanda aka fi sani da Karkuzu Na Bodara gida biyo bayan hira da Zinariya ta yi da dattijon yana neman tallafin jama’a bayan makanta da ta same shi.

Ahmed Musa   ya cika Alkawari, ya siya Wa Baba Karkuzu Gida Da Kyautar 500K (cikin hotuna)
Alkawali ya cika

Bayan kiran Zinariya nan take Ahmed Musa ya amsa tare da bada umarnin a nemawa Karkuzu gidan miliyan 5 a siya mishi domin ya tsuguna da iyalansa. Nan take wakilin Ahmed Musa Abdullahi Rocky Boy Isma’il da wakilan Zinariya suka bazama inda aka siyawa Karkuzu gidan miliyan 8 a layin Haruna Hadeja Dake Jos. Nan take Ahmed Musa ya bayar da miliyan 5.5 da Kuma kyautar 500K domin cefane Wanda ya kama miliyan 6.

Ahmed Musa   ya cika Alkawari, ya siya Wa Baba Karkuzu Gida Da Kyautar 500K (cikin hotuna)
Ahmed musa Allah ya saka da Alkhairi

Bayan, haka, bayin Allah masu taro da sisi sun tallafawa Baba Karkuzu da zunzurutun kudi da ya kai Naira miliyan 2 da motsi.

Gidan ya kunshi dakuna “safe contain” guda 2 da “single” 3 da “kitchen” da bayan gida.

Saboda farin ciki da irin tallafin da ya samu, Karkuzu ya kasa rike farin cikin shi yayin da ake mika mishi takaddun gida inda ya fashe da kukan dadi tare da addu’o’in alkhairi ga bayin Allah da suka shiga lamarin shi. Karkuzu yayi godiya ga dukkan wadanda suka tallafa mishi tare da addu’o’i da dukiyar su.

Ga Mallam Abdullahi Karkuzu nan ya karbi takaddun gida tare da iyalansa. Ga Kuma hoton gidan nan da takaddun gidan nan an damka mishi.

Ga lambar waya da account number ga duk Wanda yake son taimakawa Karkuzu ko kiran shi.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button