Labarai

Bidiyo yadda wata shantaleliyar budurwa ta mokaɗe bayan samun juna biyu ya jawo cece kuce

Wata mata mai ɗauke da biyu ta sanya wani bidiyo a manhajar TikTok domin nuna yadda jikinta ya sauya lokacin da ta samu ciki.

Bidiyo yadda wata shantaleliyar budurwa ta mokaɗe bayan samun juna biyu ya jawo cece kuce
Bidiyo yadda wata shantaleliyar budurwa ta mokaɗe bayan samun juna biyu ya jawo cece kuce

A ranar 7 ga watan Janairun 2023, Dr Teddy Sola ta sanya bidiyon wanda ya nuna yadda junan biyu ya sanya jikinta duk yayi laushi. Jaridar dimokuraɗiya ta rahoto.

A cikin ɗan gajeran bidiyon mai tsawo daƙiƙa 14, Teddy ta nuna tsofaffin hotunanta da kuma sababbi lokacin da take zaman jiran tsammanin haife abinda ke cikinta.

Tsofaffin hotunan sun nuna Teddy lokacin tana kyakkyawa, ƴat siririya sannan ga ƙwalisa.

Sai dai, abubuwa sun sauya lokacin da ta samu juna biyu domin jikinta ya fara samun baƙin al’amura waɗanda da babu su.

Hakan ya zo da sauye-sauye masu yawa waɗanda suka sanya ta koma da ƙyar ake iya ganeta yayin hancinta ya kumbura.

A cikin hotunanta lokacin da take da juna biyu, Teddy tayi baƙiƙƙirin saɓanin da yadda take da haske.

An kalli bidiyon sama da sau dubu ɗari huɗu sa arba’in da tara a TiktTok. Wasu daga cikin waɗanda suka kalli bidiyon har shakku suka nuna cewa ba ita bace a cikin tsofaffin hotunan.

@dr_teddysola Pregnancy will humble you ???? #viral #reels #fyp #explore #pregnantlife #pregnanttiktok #makemefamous #explorepage @yabaleftonlinemedia @gossipmill @pulsenigeria247 @mufasatundeednut @biesloaded @donjazzy ♬ RMX CHORAL CDM MONEY SONGS BEAT X ELTON BOY BEATZ – vibe for the whole Planet????????

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button