Labarai

Kabilar Himba: Wacce namiji ke karrama bakonsa ta hanyar ba shi danin matarsa don more dare

Can yankin Kunene da Omusati da ke arewacin Namibia, akwai wasu jama’a makiyaya ‘yan kabilar Ovahimba da Ovazimba, Pulse.ng ta ruwaito.

A al’adarsu, a ko wacce rana mace za ta dinga tatsar nonon shanu tare da kulawa da yara, yayin da mazan su ke fita farauta har su dauki tsawon lokaci.

Iyayensu maza ne ke zabawa mata mazajen aure

Amma a ka’idar kabilar, namiji ne kadai mai zabi. Mace kuwa kusan za a ce ba ta da ta cewa da rayuwarta. Wajibi ne ta yi biyayya ga mijinta.

Kamar yadda Labarunhausa ta ruwaito, idan aka yi bako namiji, ana karrama shi ne ta salon Okujepida Omukazendu – wato namiji ya bar wa bakon danin matarsa da dare yayin da mijin zai koma wani dakin na daban.

Idan kuma babu daki, wajibi ne ya hakura ya kwana a waje.

Su na yin hakan ne don kishin maza ya ragu sannan a gwada juriyarsu.

Su na sanya dokar hana wanka

Dayar al’adarsu wacce yanzu aka dena yin ta ita ce dokar haramta wanka.

Maimakon mata su yi amfani da ruwa wurin wanka, su na turara jininsu ne yayin da su ke shafa wani mai na musamman(kalar ja).

Sun yarda da cewa jar fara tana da matukar kyau da daukar hankali kuma sun yarda da cewa man da su ke shafawa ya na kare su daga rana da cizon kwari.

Mutanen Himba ba su wani samu damar shiga littafan tarihi da al’adun nahiyar Afirka ba.

 

Akalla sun kai mutane 50,000 a yankin kuma su na auren mata fiye da daya yayin da ake aurar da ‘yan matan Himba ga mazajen da iyayensu su ka zaba musu da zarar sun kai munzalin balaga.

Sai dai yanzu sun rage wasu daga cikin al’adunsu saboda zuwan boko yankin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button