Wata jami’a a Amurka ta kori farfesa bisa nuna zanen Ma’aiki
An kori wata farfesa a jami’ar Hamline ta Minnesota da ke Amurka, Erika López Prater bayan samun ta da lefin nuna hotunan zane na Annabi Muhammad (SAW) ga dalibai yayin wata lacca.
Daily Nigerian Hausa na ruwaito A cewar rahoton, wata ɗaliba ce ta kai ƙara ga hukumar jami’ar kan hoton.
Ɗalibar, Aram Wedatalla, ta shaida wa wata jaridar makarantar a watan Disamba cewa nuna hoton raini ne gare ta.
“Ina jin cewa anya wannan abin da a kai min ma gaske ne kuwa,” in ji ta.
Wedatalla, yar kasar Sudan, ta kara da cewa ba za ta taba kasancewa cikin al’ummar da ba a mutunta kimarta ba.
“A matsayina na musulma kuma bakar fata, ba na jin kamar na zama, kuma ba na tunanin zan taba shiga cikin al’ummar da ba sa daraja ni a matsayina na yar cikin su, kuma ba sa girmama ni kamar yadda na ke girmama su. irin girmamawar da nake nuna musu,” ta kara da cewa.
Yayin da take kare kanta, malamar, ƴar shekara 42, ta ce ta yi taka-tsan-tsan kafin ta nuna zanen na Annabi a karni na 14 ga wani rukunin tarihin fasaha na duniya, a cewar rahoton The New York Times.
Prater ta ce sai da ta yi gargadi a cikin manhajar karatun ta cewa za ta nuna hotunan mutane masu tsarki, da suka hada da Annabi da kuma Buddha, a cikin karatun.
Ta kuma bukaci dalibai da su ke da wata suka a kan hakan da su tuntube ta amma babu wanda ya yi hakan.