Labarai
Garabasa ! Duk Wanda Ya kawoshi Zai Samu Kyautar Naira Miliyan Biyar ₦5M
Advertisment
Rundunar ‘Yan sandan Jihar Katsina, tace zata bayar da ladar Naira Milyan Biyar (5,000,000.00) ga duk wanda ya bada bayani akan yadda za’a kama Adamu Aliero ko kuma ya kawo gawarsa.
Adamu Aliero wanda shine jagoran wadanda suka kai hari a garin Kadisau na Karamar hukumar Faskari ta Jihar Katsina, harin da yayi sanadiyyar kashe sama da mutane 20.
Adamu Aliero ‘dan asalin Kauyen ‘Yan-kuzo ne na Karamar hukumar Tsafen jihar Zamfara, kuma ya hada kai da manyan ‘Yan ta’adda ne domin kai hari a kauyen Kadisau.
Kamar yadda Kwamishinan Yan sandan Jihar Katsina ya bayyana, yace bayanai sun nuna cewar Aliero ya kitsa kai harin ne saboda ‘Yan sanda suna rike da ‘Dansa mai suna Suleiman, kamar yadda zakuga hoton Adamu Aliero da ‘Dansa Suleiman
To al’umma sai a bazama neman wannan gawurtaccen ‘dan ta’adda Adamu Aliero a kawo shi a mace ko a raye domin samun wannan babbar lada ta Naira Milyan Biyar (5,000,000.00)
Allah Ya bada sa’a
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com





