Labarai

Musulma ta raba kayan abinci, atamfofi da kuɗi ga mata kiristoci 50 a Kaduna

A wani bangare na bikin Kirsimeti na bana, wanda ya zo a cikin tashin farashin kayayyaki, a fadin kasar, wata mata musulma, Ramatu Tijjani, ta sake raba kayan abinci da zannuwa da kuma kyautar kudi ga zawarawa Kiristoci 50 a jihar Daily Nigerian Hausa na ruwaito.

A cewarta, ta ƙissima za ta raba wa zawarawa sama da 200, tana mai cewa hakan wani bangare ne na kokarin inganta zaman lafiya a tsakanin addinai daban-daban.

Musulma ta raba kayan abinci, atamfofi da kuɗi ga mata kiristoci 50 a Kaduna

Musulma ta raba kayan abinci, atamfofi da kuɗi ga mata kiristoci 50 a Kaduna
smart

Ta ce an bayar da kyaututtukan ne da nufin sanya musu farin ciki a fuskarsu ta yadda za su kula da marayun su da kuma ba su damar gudanar da bukukuwan cikin farin ciki da jin dadi kamar sauran Kiristocin duniya.

Tijjani ta bayar da gudummawar ne a cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry, Sabon Tasha, a jiya Lahadi a Kaduna.

A cewarta, gudummawar ta samo asali ne daga sha’awarta da kuma buƙatar yin tasiri ga rayuwar zawarawa marasa galihu waɗanda suka sha wahala da wariya har ma sun fara fitar da rai da rayuwa.

Ta ce tun shekaru 10 da suka gabata, tana bayar da gudummawar buhunan hatsi, kayan sawa da lemukan sha ga zawarawa Kiristoci da marayu a lokacin Kirsimeti, da bukukuwan Ista da nufin karfafa dangantakar Kiristoci da Musulmi a yankin Arewa.

Musulma ta raba kayan abinci, atamfofi da kuɗi ga mata kiristoci 50 a Kaduna

Musulma ta raba kayan abinci, atamfofi da kuɗi ga mata kiristoci 50 a Kaduna

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, matan kiristocin sun kira Tijjani da “Mama” ne saboda kyakkyawar alaka da ta kulla da su wajen karfafa alaka tsakanin Kirista da Musulmi a jihar da ma kasa baki daya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button