Labarai

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana
Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yakibda yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC akan zargin da yake yi mata da almundahana da kuka azurta kanta ta hanyoyin da basu dace ba.
Daily Nigeria ta ruwaito tuni hukumar EFCC ta aikewa da Hafsat Ganduje mai dakin Gwamnan Kano da goron gayyata domin amsa tambayoyi kan zargin amma taki amsa gayyata, ba kuka tare da ta bayar da wani uzuri a rubuce ba.
A cikin wasikar da Abdulaziz Ganduje ya aikewa da EFCC ta shafi badakalar filaye da kuma kudade. Sai dai kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren yaki cewa komai gake da batun da aka yi masa tambaya akai.
Idan ba a manta ba, a baya an zargi Gwamnan Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje da yin badakala ta sama da dalar Amurka miliyan biyar, inda aka nuno shi a wani faifan bidiyo yana karbar dalar Amurka daga cikin kudaden ‘yan kwangila, Gwamnan dai ya karyata bidiyon tare da kai karar jaridar Daily Nigerian da mawallafinta Jaafar Jaafar gaban kotu game da batun bidiyon Dala.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button