Kannywood

Martani zuwa ga Sadiq Sani SadiQ da yan fim – Sheikh Bashar Ahmad Sokoto

Advertisment

Bayan maganar Dr idris Abdul’aziz Bauchi da yayi akan yan fim cewa dukka su basu da addini inda wannan maganar ta jawo cece kuce sosai inda su yan fim din na mayar da raddi wasu kuma sunka nuna goyon bayansu inda har wani jarumi yayi ikirari cewa shi har tashin Mahadi yana nan a cikin harka fim har ya tashi a gaban Allah ya matsahinsa dan fim haka yake fata.

Sheikh Bashir Ahmad sani Sokoto yayi martani ga wannan jarumi tare da dukkan jaruman kannywood da nasiha a cikin wannan martani ga abinda babban shehin malamin islama a Nijeriya yake fadi.

Martani zuwa ga Sadiq Sani SadiQ da yan fim - Sheikh Bashar Ahmad Sokoto
Martani zuwa ga Sadiq Sani SadiQ da yan fim – Sheikh Bashar Ahmad Sokoto

Kai gashi baka gamsu baka yarda ba an karanta ma Ayar Allah kayi girman kai kuma gashi ka fito kana mayar da raddi har tashin Mahadi ka mutu kana fim ka shi gaban Allah a matsayin dan fim nikam ban maka wannan fatan Allah ya gafarta maka ka mutu kana cikin sojoji as sadikul Akbar ka mutu ka tashi rike da hannun manzon Allah s.a.w ina maka fatan ka gyara kada zafin kalma da wani malami ya fada maka kayi amfani da wannan ko wasu masu zugi su zugeka kazo kana irin wannan abu.

Idan wani malami yace muku baku da addini ku nada daligate kuje inda yake akarmukallahu kace bamuda addini minene shi mu kaffirai ne ko musulmai amma wadanda basu riko da addini saboda kalma nada harshen damo idan ya fasara sai kuce Akarmukallahu so muke ayi mana gyara ya zamuyi mu gyara yanzu kuma mungode da wannan nasiha da kayi mana amma kalma da kayi amfani da ita duniya zatayi Mana dauka kafirai akarmukallahu muna kira muna roko a gyarata ayi kira ta wata hanya ayi amfani da wata kalma wadda bata da harshen damo kaga shikenan.

Advertisment

” Shi da kasan da yaji yasan yana magana da wadanda sunka san kansu Sa’a nan kunyi abinda ya dace na hakkin ku kun saukar dan haka nike kira da babba murya ina Ali Nuhu yake so ina kira gareka da babba murya ,ina sani danja yake ina kira gareka da babba murya, ina Adam A Zango yake ina kira gareka da babba murya , ina SadiQ sani SadiQ sunan ko as sadikul Akbar ke gareka don Allah ka gyara wannan maganar taka kayi kwaikwayo da as sadikul Akbar.

Ku manya ne ko ince mutane ne a cikin ku akwai yara a wannan harka akwai wani na nan mai waka ado Gwanja da sarkin waka nazir da dukka dai iri irensu ina kira garesu da babba murya, idan irin wannan matsala ta tashi ku riga dauka matakin da ya kamata matakin maida raddi da cin mutunci ba daidai ba ne Sa’a nan sana’ar nan taku tana da kura kurai cikinta wadda asalin gininta ma ba halal bane kuyi kokari ku nemi wata sana’a , Sa’a nan akwai haram da yake sandararen haram akwai kuma haram mai naso fim haram ne mai naso wanda idan ka aikata bai tsaya nan ba yanzu in nichi haram ya tsaya nan ko in niyi wani abu ya tsaya nan gareni to shi idan kayi wani ya saurara kana da laifi duk wanda yayi kwafiyin ya aikata abinda kayi kana da laifi ilah yaumul kiyama ma’ana har tashin duniya.’

Ga sauran bayyanai ku saurara daga bakinsa.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button