Kannywood
Ana kashe mu a arewa amma an kasa samun masu fitowa suyi magana – Hadiza Gabon
Fitacciyar jarumar Kannywood Hadiza Gabon, ta nuna takaicinta kan abin da ta kira yadda ‘yan Arewa suka kasa nemar wa ‘yan uwansu hakki yayin da takwarorinsu na Kudu suke ta fafutikar nemar wa nasu ‘yanci.
Hakan dai na zuwa ne yayin da mutane da dama a shafukan sada zumunta ke ta kokawa kan yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ƙamari a arewacin Najeriya.
Ta nuna irin yadda yaro daya anka kashe amma yan legas sunka fito sunkayi zanga zanga wanda har buhari yaje legas yayi musu alkawalin za’a yi sahihin bincike.
View this post on Instagram