Fitaccen marubucin Datti Assalafy ne ya wallafa wannan rubutu a shsfinsa inda ya fadi cewa babban shein malamin ya lissafa laifuffukan yan fim wanda suke aikatawa fim sun hada tun daga na kannywood har zuwa india fim malam yace ba yan kannywood ba a fahimmci kalmar ga abinda ya wallafa.
“Babban Malamin Musulunci dodon marassa gaskiya da ‘yan bidi’ah Ash-sheikh Dr Idris Abdul-Aziz Bauchi ya taro fada da dillalen shaidan wakilan yahudawa masu bata tarbiyya wato ‘yan Fim
A yanzu Malam ya fara da zayyano abubuwa guda dari (100) na haram wanda ‘yan Hausa fim suke aikatawa
A Khudubar juma’a da Malam ya gabatar jiya, yayi magana akan abubuwa 24 cikin 100 na haram da ‘yan fim suke aikatawa, gasu kamar haka:
1. Rashin Jin kunya (haramune)
2. Karya a maganganunsu
3. Kadaita da matan da ba muharramansu ba
4. Haduwan mata da Maza
5. Rawa da waka
6. Waka
7 Kida
8. Shiga wanda ya sabawa addini
9. Baiyana al’aura
10. Firm Yana jawo saki tsanin ma’aurata
11. Yin ado badon miji ba
12. Tafiye-tafiye ba da muharrami ba
13. Sabawa iyaye
14. Zagin iyayen juna
15. Kalmomin batsa
16. Bayyana barna a fili
17. Tayarda sha’awa
18. Suna sawa ayi Zina
19. Suna sawa ayi fyade
20. Koyar da sata
21. Gulma
22. Annamimanci
23. Basaja
24. Hassada
Sauran abubuwa na haramci 75 da ‘yan fim suke aikatawa suna tafe Insha Allah, na rantse da Girman Allah ‘yan fim sun taro fadan da ba zasu iya ba, Malam zai yi nasara a kansu
Ban taba ganin wanda yayi fada da Malam Idris Abdul-Aziz Bauchi ya kai labari ba, domin Wallahi Malam Idris akan gaskiya yake, shiyasa Allah Ya ke taimakonsa akan mabarnata da sauran mutanen banza, zagi da kamu da barazanan kisa baya tasiri akansa
Zan tura audio wannan khuduba a cikin bidiyon da munka kawo muku a kasan posting namu sai a saurara.
Muna rokon Allah Ya kare mu da iyalan mu daga sharrin ‘yan fim”