Kotu ta aike da Mubarak Uniquepikin gidan yari bayan sukar Ganduje a Comedy


Kotun Majistiri mai lamba 58 da ke Nomansland a Kano ta aike da wasu matasa masu wasan barkwanci zuwa gidan yari.An gurfanar da matasan ƴan wasan Barkwancin Mubarak Muhammad da aka fi sani da Uniquepikin da mai ja masa baƙi Nazifi Isah Muhammad a gaban Kotun bisa zarge-zarge guda huɗu.
Hukumar tace fina-finai ta Kano ce ta yi ƙararsu bisa zargin haɗa kai, da ɓata suna da cin zarafin Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje tare da yunƙurin tayar da hayaniya a wani faifan bidiyo da suka fitar.
Yayin zaman Kotun na yau Laraba waɗanda ake zargin sun amsa tuhumar da ake musu.
Lauyan da ke kare su da iyayensu, sun roƙi kotu da ta yi musu afuwa.
A nan ne kuma alƙalin Kotun mai shari’a Aminu Gabari ya ɗage shari’ar zuwa ranar Litinin 7 ga watan Nuwamban da muke ciki.
Hankalin “Yan Tiktok Ya Tashi Bayan Kama Mubarak
Fitaccen mai wasan barkwancin nan a sahar Tiktok Mubarak UniquePikin ya shiga komar Gwamnati,domin yanzu haka yana gidan dan kande a tsare bayan zagin tsamar nama da yayiwa Gwamnan jihar na Kano tare da iyalansa baki daya.
Ga duk mai bibiyar dandalin yasan Mubarak da kuma irin Shirin sa da yake yi tare da Kaninsa wanda yake kira da Na’ibi.
Hankalin “Yan Tiktok Ya Tashi Bayan Kama Mubarak
Bayan Mubarak din yana tsare a wajen hukuma dubban “yan uwa da Abokan Arziki ne suka dinga taya jaje tare da mika kokon bara zuwa Gwamnan na jihar ta Kano domin yayi masa afuwa sannan a sako musu dan uwa.
Cikin wadanda suka mika kokon barar sun hada da manyan Abokan sa a sahar irin su Baddo (Ali Nuraddeen),Murja Ibrahim Kunya,MJ Talent,Abba C Sale da dai sauran su.
Ba tare da bata lokaci ba zaku iya kallon cikakken bidiyon anan kasa.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





