Labarai

Dalilan Da Suke Hana Wasu Matan Sha’awar Jima’i

A lokacinda wasu matan shaawarsu na son yin jima’i ya fi karfin mazajen su, akwai kuma wasu matan da mazajen su na fama dasu ne saboda yadda basuda sha’awar yin jima’i Sam.
Irin waɗannan matayen a kullum suna samun matsala da mazajen nasu wanda hakan yasa wasu masu irin wannan matsalar suke dauka ko an musu asiri ne ko kuma dai suna dauke da wata cutar ne.
Eto ana iya samun duka biyu, sai dai kuma akasarim mata masu wannan matsalar babu wata cuta ko asiri da aka musu domin a dauke musu sha’awar su.

Dalilan Da Suke Hana Wasu Matan Sha'awar Jima'i
Dalilan Da Suke Hana Wasu Matan Sha’awar Jima’i

Ana samun wasu mata da haka nan halittar su yake na basu da sha’awar yin jima’i kamar yadda ake samun wasu matan masu tsananin sha’awa. Sai dai kuma kamar yadda masu illimin jima’i suka gano. Kashi 1 ne kawai cikin 100 na matan da ba a cika samun su da sha’awar jima’i ba. Don haka akasarin mata masu fama da irin wannan matsalar da akwai wasu dalilai da suke hanasu sha’awar jima’i kamar haka:
1: Rashin son mijin da suke aure. Mace ba kamar namiji bane. Idan har bata son mijin da aka aura mata duk yadda zai taba ta sam bazata ji wani sha’awar ya motsa mata ba.

Shi kuwa namiji ko baya son mace muddin har zai amince ta taɓa shi, tana iya motsa masa sha’awar sa har ma ya biya mata bukatar ta.
Don haka idan kina da wannan matsalar sai ki duba shi mijin da kike aurensa ko akwai soyayya a tsakaninku. Mace idan tana son mijinta wata ko muryrasa ko da tunaninsa ta yi sha’awar ta zai iya motsawa.
2: Rashin Kwanciyar Hankali – Bama ga mata ko maza muddin hankalin su ba a kwance yake ba to babu da wani sha’awar yin jima’i da matansu. Hakan wannan matsalar ma take da mata. Muddin mace bata da natsuwa akwai wani muhimmin abunda ke damun ta kuma ya tsaya mata a rai, nan take sha’awarta yake daukewa.

3: Shan Miyagun Kwayoyi- suma suna daukewa mace sha’awar ta na jima’i. Haka shima yawan shan taba sigari.
Duk macen da take mu’amala da miyagu kwayoyi kuma sama da rabin lokacinta tana buge. Irin waɗannan matan basu da wani sha’awar jima’i a tare dasu. Shi yasa ko yan matan da suke yawan shan kodin zina bai damesu ba. Su dai suyi dip kawai. Idan ma ta kama zasu yi jima’i suna yi ne domin shi mai bukatar ya gamsu amma ba dominsu ba.
4: Cuta – Akwai cuttutuka irin na hawan jini, ko ciwon shuga cuttutuka ne da suke daukewa mace sha’awar ta na jima’i muddin yayi kamari a jikin su. Kamin har sha’awar su ya dawo sai sun samu sauki. Haka ma ciwon mata na fibroid shima yana daukewa Mata sha’awar su ta jima’I.

5: Shekaru- Karancin shekaru da kuma yawan shekaru na hana mace sha’awa.
Akwai matan da ake aurar dasu da karancin shekaru irin waɗannan suna yin jima’i ne kawai amma ba wai domin suna sha’awa ba. Haka nan matar da shekarunta suka ja ita ma sha’awanta na iya daukewa.
Waɗannan sune wasu daga cikin abubuwan da suke haddasawa mata daukewar shaawarsu na jima’i.
A darasi na gaba zamu kawo hanyoyin magance su.
#tsangayarmalamMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button