Labarai

Bello Yabo Yayi Martani mai Zafi kan Buhari Akan Chanza Kudi

A yan kwana kin nan da ake ta cece kuce akan chanza kudin Nigeria da za’a yi wanda kowa yana tofa albarkacin bakinsa wanda kowa yana hasashen cewa tabbas za’a yi hasara sosai, wasu na cewa wannan chanza kudin zai kawo durkushewar tattalin arzikin arewacin Nigeriya saboda yawancin yan arewa mazauna kauye zasuyi hasara sosai da sosai wasu na cewa a’a ae wasu manya manyan yan kasuwa da yan siyasa ne suka tara kudi a gida jibge wanda idan ankayi wannan chaza kudi zasuyi hasara.

Bello Yabo Yayi Martani mai Zafi kan Buhari Akan Chanza Kudi
Bello Yabo Yayi Martani mai Zafi kan Buhari Akan Chanza Kudi

Ash sheikh Bello Aliyu Yabo Sokoto yayi tsokaci sosai akan wannan chanza kudi da za’a yi inda ya kawo tarihin yadda ya Chanza kudin nigeria a lokacin da ya karbi mulki soja mallam yayi bayyani dala dala.

Wai chanjin kudi ! Kun tabbatar da tuwo bai Chanza sunai 1984 haka yayi fa kuma yaga abinda ya faru ga Nigeria ga ba daya da mutanen Nigeria da tattalin arzikin Nigeria shine chanjin kudin nan sanadiyar karewar tattalin arzikin Nigeria.

Yara kuke kuje ku samu dattijai irinmu ku tambayesu kafin buhari idan mutum zaije hajji, alhazzai mu na Nijeriya idan zasu tafi hajji babu ruwansu da chanjin kudi ka sanya ko nawa gareka ka tafi dasu Makkah ana amsa duk inda kaje ana amsa kudin Nijeriya sai yazo ya Chanza kudi cikin dan lokaci kankane shikenan bakin date line yana cika duk wani mai bakin magana ina tuna har margayi mai martaba sarkin musulmi Abubakar na ukku yayi magana yace dan Allah a kara lokaci yace ko minti guda ba’a karawa kuma ko bana haka za’a yi.

“Naji wasu malamai suna ta kiraye kiraye suna ta rokonsa nace kun ɓata lokaci bakusan mutumin ba shiyasa wai ka ayi ae an wuce wurin tunda har an bugo kudin ko baku gani hotunsu ba. An kashe biliyoyin kudi kuma kace ka ayi ,in ba’a yi ba ya za’a yi da kudin da anka bugo ae magana ka’ayi bata taso ba hmm.

“Sa’a nan duk lokacin da anka sa kuma bai kara ko kwana gudu haka ankayi ko wancan lokaci 1984 mutane sun kayi ta hasara bakin lokacin duk wanda bai chanza ba to wannan kudin basu da banbanci da sansanmin leaf mutane da nan gida da waje sunkayi hasara mai yawa tun lokacin nan kasashe sunka daina karba kudin Nijeriya. Sa’a nan nan mutane da yawa anka jawa asara.

“Naji wani malami lawal Abubakar Shuaibu kano yana bayyani cewa wasu mutane ne yake targeting suna nan sun tara kudi dan haka bari ayi chanjin kudi suyi asara malam lawal yace wadannan da kake targeting ko anyi chanjin kudi ba sune zasuyi asara ba wadanda baka zato talakawa bayin Allah sune zasuyi asara wadanda sunka wahala sunka samu kudi wadanda sunka haka don ka kai sune zasuyi asara.

“Mafi yawan wadannan da kake targeting duk mafi yawan masu aikin banki yaran su ne.

Malam ya kara da cewa sa’a nan yanzu misali ina da naira billiyan biyar sai inkira manajan banki manaja eh dan Allah ga kudi na nan kun fara chanji eh ga billiyan biyar dina nan a chanzamin okay to ya za’a yi zan baka naira miliyan dari ukku  kai da yaranka shin kana ganin shekara nawa zaiyi kafin ya samu wannan kudin? Bai chanjamin in kaje da naira dubu dari zai dube ka to saboda haka basu zasu asara ba.

“Talakawa nan sune zasuyi asara masu noman tanka, noman rani da sauransi sune zasuyi asara haka za’ayi tayi kuje banki tun da safe har maraice ace ku dawo gobe har date line ya cika shikenan anka barsu da buhu huwa sun zama shara shi a sanadiyar karewar mutane.

Sa’a nan yaji iri ɓacin/zagi da ankayimai lokacin kuma yasan irin yadda tattalin arzikin Nigeria da yan Nijeriya sunka shiga amma dan kusan tuwo ba’a chanza mai suna.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button