AddiniLabarai

YANZU-YANZU: Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, Ya Sanar Da Ganin Jinjirin Watan Ramadan A Najeriya

Mai alfarma sarkin Musulmi yayi sallama irinta addinin inda ya tabbatar da yau 29/8/1443AH ranar karshe wannan wata
Sarkin Musulmi yace gobe 2 ga watan April itace daya 1 ga watan Ramadan, kamar yadda kwamitin ganin wata ya tabbatar cewa anga jinjirin watan Ramadan a cikin sasasan kasar nan kamar haka:-
WURNO
ZAMFARA
YOBE
KADUNA
KANO
PLATUE
Saboda Haka Gobe Asabar Itace 1st Ramadan, 1443AH.
Mai alfarma sarkin Musulmi ya roki Allah ya bamu albarkacin wannan wata da falalar da ke cikinsa tare da yan uwa musulmi su yaiwa addu’a ga wannan kasar musamman arewa domin samun zama lafiya.
Mai Alfarma Sarkin musulmi yayi kira ga masu hannu da shuni ma’ana masu hali da su taimakawa al’ummar da suke bukatar taimako musamman yan gudun hijira.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button