Jirgin Yakin Nigeria Yayiwa Maboyar Yan Ta”adda ruwan wuta a zamfara
PR Nigeria ta ruwaito cewa Yan”taaddar yaran shugaban Yan bindiga halilu tubaline.Halilu sububu Wanda akewa lakabi da shugaban Yan ta”addar Africa Wanda yakeda zama A maradun ta jahar zamfara.
Halilu, anyi ittifakin shine Dan ta”addar da yake samawa sauran yanta”addar dake jahohi makwabta makamai, Halilu yafi kowane Dan ta”adda arziki a yankin zamfara Katsina da sauran jahohin arewa maso yamma.
Yana yawan gudanar da aikinsa na ta”addanci wajejen Sububu, Anka (Bayan Daji) da Kuma Bayan Ruwa a jahar ta Zamfara, ankuma tabbatar da shine ke Kai hare haren satar dabbobibi da satar mutane domin naiman Kudin fansa a wannan yankin.
Jirgin yakin na Nigeria dai yayiwa Yan”taaddar yaran halilu sububu kisan kiyashine lokacin da aka samu bayanan sirri dake nuni da cewa Halilu yakira Taron tattaunawa da wasu mayakansa a wajen da yake Adana makamansa a karamar hukumar Maradun ta jahar zamfara.
Wani shugaban sajo ya gayawa PR Nigeria cewa bayanan sirri sun gano idan sububun yake Adana makamansa da motoci,harsassi da sauran kayan sata.
Shugaban sojan ya Kara da cewa bayan satittikka da kwanakki da akayi ana bibiyarsa ta bayanan sirri ranar 21 October 2022, Jirgin yakin sojan yayiwa maboyar tasa tsinke inda yayiwa magoya bayansa kisan kiyashi har kimanin su fiye da talatin.
Yayin harin harin matukin Jirgin yagano dunkulen wata ya tashi awurin da yakai harin inda ake tsammanin tarin bomabomaine.
Babu tabbacin koshi sububun na cikin wadanda harin ya rutsa dasu Amma dai mazauna kauyukkan sun tabbatar da kissan.
Mustapha sarkin kaya.