Labarai

Yadda Zaki Sace Zuciyar Masoyinki Ta Hiran Text

Sakon text kai tsaye ko ta WhatsApp ko ma DM. Hanyace yanzu haka da masoya suke hira cikin sauki.
Sai da kuma ba duk ‘yan mata bane suka iya yin hiran da zasu jawo hankalin masu sonsu ta wadannan hanyoyin ba.
Wasu matan ana fara hira dasu zasu sako maganar da zai iya batawa masoyinsu rai, wasu basu da kalaman da zasu iya jawo hankulan masu sonsu.

Ga wasu hanyoyin da zaki iya shawo kan masoyinki dasu ya rika yin marmarin son hira dake.

1: Ki Jira Shi- Kada kiyi saurin soma tura masa sakon text, ki bari har sai shi da kansa ya soma sannan ke kuma ki maida masa.

Idan kika bashi lambarki a karon farko ko haduwar farko, ki daure duk irin zakuwar da kikayi har sai shi da kansa ya soma yi miki magana.
Wannan dabara ce dake sa masoyinki yaji cewa baki da arha baki da sauki ba kuma neman kai kike da kanki ba.

2: Kada Ki Amsa Shi Duka- A kullum idan masoyi ya miki tambaya da ya wuce 2 a text ki amsa guda daya kawai ki tsallake sauran.

Hakan zai sa ya zaku ci gaba da hira dake domin nacin son jin sauran tambayoyin da baki amsa masa su ba. Idan har ya dameki da son jin su, nuna masa a hiranku na gaba zaki bashi amsa, wannan zai jawo hankalinsa ya nemi yin hira dake a duk lokaci.
3: Ki Soma Da Gaske- A sakonki na farko ga sabon masoyinki kada kiyi gutun rubutu. “Yaya kake, yaya gari, ko Salam” duk wannan kauyanci ne. Sake masa zancen sosai yadda zai ji ya saki jiki dake ya dace da macen aure ya samu masoyiyar data iya soyaya.

Ganin wannan sakon naki zai sa cikin rawar jiki sai ya sake turo miki wani sakon. Sai dai a wannan karo kada ki ce masa uffan shiga harkokin ki manta dashi. A hakan ne zai sashi matsuwar son ganin da karanta duk wani sakonki. Zaki sashi cikin zullumi da kokwanto tunanin anya kece kuwa ma kika tura masa sakon farkon kuwa. Da wannan wasiwasin zai kasance cikin son yin hira dake.

4:Sakon Soyaya- ki tura masa sako na soyayya koda kalma dayace ko kuma emoji dake dauke da harkar soyayya.
Kada kiyi hakan da sakon wani rubutu daga gareki mai tsawo. Kawai kalma guda rak, ko hoton guda daya sai ki kama bakinki kiyi gum.

Wannan yana yiwa masoyi tasirin da kuma fidda shakku da kokwanton soyayyar da kike masa.
Shi sabon masoyin idan kina son masa tarko ta hanyar sakonnin text, kada ki yawaita masa magana amma ki yawaita yi masa tambaya. Kada kuma a makon farko ya fahimci sonshi kike ko dai har yanzu bai samu shiga ba ta hanyar takaita sakonninki gareshi.
5: Yi Kokarin Kawo Karshen Hiranku- Idan kuna hira kada ki zama kece mai tada hiran idan yayi shuru. A ko yaushe ki rika barinsa ya rika aikin hira. Idan hira ya zo karshe kiyi shuru kiga zai tayar da hiran kodai an gama kenan.
Idan an samu mintuna a tsakanin kamin ya sake motsa hiran kada ki bashi amsa ko masa bayani nan take, bada dan rata kadan kamin ki yi wani sakon.

Wadannan wasu ne daga cikin dabarun jawo hankalin masoyi musamman sabbin maza ta hanyar hira ta text.
Dabarune da namiji zai rika marmarin son hira dake ba tare da ya zaku ba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button