Labarai

Za a rinƙa cilla wa ‘yan gudun hijira abinci daga jirgin sama ~ Sadiya Farouk

Advertisment
Za a rinƙa cilla wa ‘yan gudun hijira abinci daga jirgin sama
Gwamnatin Najeriya ta fara shirye-shiryen bayar da agaji ga ƙauyukan arewa maso gabashin ƙasar ta hanyar amfani da jiragen sama domin cilla wa ‘yan gudun hijira abinci.
Ministar kula da ayyukan jin-ƙai da kare afkuwar bala’i Sadiya Farouk, a ranar Lahadi ta shaida wa ‘yan jarida a Maiduguri cewa za a fara amfani da jiragen sojojin saman Najeriya domin cilla abinci da sauran kayayyakin tallafi kamar bargo da dai sauransu ga ‘yan gudun hijira.
Ta bayyana cewa akwai matsaloli da ma’aikatan bayar da agaji ke fuskanta na kai wa ga jama’ar da ke cikin ƙauyen ƙayau, inda ta ce cilla abincin ne mafita ga ƙauyukan da mota ba ta iya zuwa.
Bbchausa sun kara da cewa yankin arewa maso gabas na daga cikin wuraren da rashin tsaro ya fi ƙamari a Najeriya.
Dubban mutane aka kashe tun bayan fara rikicin Boko Haram a yankin tare da raba miliyoyi da muhallansu.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button