Labarai

Faransa ta halasta zubar da ciki

Advertisment

Faransa na shirin zama kasa ta farko da ta fito karara ta sanya dokar zubar da ciki a cikin kundin tsarin mulkinta,sabanin kasashe da dama da ‘yancin zubar da cikin ke raguwa.

Wakilaina ‘yan majalisar dattijai na shirin kada kuri’a da gagarumin rinjaye su amince da gyaran kundin tsarin mulkin da gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ta gabatar.

Dw hausa ta ruwaito cewa,masu adawa da zubar da cikin sun ba da sanarwar yin wani gangami a Versailles, yayin da magoya bayan sauye-sauyen zasu yi taro a Trocadéro da ke a birnin Paris domin nuna farincikinsu. Hakan dai na zuwa ne kwanaki hudu kafin ranar takwas ga Maris, ranar mata ta duniya.

 

Advertisment

Wani labari : An kama masu buga kudin jabu a Spaniya

 

Jami’an ‘yan sanda a kasashen Spaniya da Italiya da kuma Girka sun kai farmaki kan wata kungiyar miyagu ‘yan asalin Pakistan da ke bugawa da kuma rarraba jabun kudade

Yan sanda sun ce miyagun sun samar da kudaden bogin da ya suka kai kimanin euro miliyan daya a takadar kudi ta euro dari-dari. Rundunar ‘yan sandan Spaniya ta ce, za a iya rarraba jabun kudaden a injinan ATM ba tare da an sani ba.

Tuni dai jami’an suka ce sun kama mutum 14 daga biranen Barcelona da kuma Rome ciki har da shugaban kungiyar.

Tun a watan Nuwamban bara ce dai ‘yan sanda suka baza komarsu bayan da aka gano jabun kudade na yawo a birnin Barcelona.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button