Kannywood

Hotunan Jaruma Dr.Girema saratu kwana casa’in da Angonta

Yadda ankayi shagalin Bikin Jarumar saratu Zazzau kwana casa'in

Saratu Zazzau, fitacciyar jarumar Kannywood wacce ta fito a fim din Kwana Casa’in mai dogon zango a Dr. Girema ta yi aurenta jiya, ranar Juma’a, 14 ga watan Octoban 2022.

Jarumar ta amarce da angonta, wanda su ka kwashe lokaci mai tsawo su na soyayya wanda sai yanzu Allah yayi za su yi aure.

Sanin kowa ne cewa jarumar ta dade tana fim, sai dai bata shahara sosai ba sai a wannan karon da ta dauki roll mai kyau a Kwana Casa’in inda tayi farin jini kwarai bayan bayyana a shugabar wata makaranta.

A kwanakin baya BBC ta zanta da ita inda ta shawarci matan da basu shiga fim ba da su dakata, kada su shiga, su je suyi karatunsu sannan suyi aure.

Ta kuma bayyana dalilin da ya sanya auren ‘yan fim ba ya karko, inda tace akwai mazan da ke kallonsu a talabijin amma kuma niyyarsu akansu ba mai kyau bace. Wannan ya sanya da zarar sun auresu, babu jimawa sai su sake su.

Auren da tayi jiya ya bai wa kowa mamaki, sai dai wakilin Labarun Hausa ya samu nasarar samun rahotanni har da hotuna ta hannun Zainab Baba Ahmed, wacce itama ta halarci bikin inda tace abu ya yi armashi.

Muna mata fatan alkhairi tare da addu’ar Allah yasa mutu ka raba. Ameen.

Ga hotunan nan .Hotunan Jaruma Dr.Girema saratu kwana casa'in da Angonta Hotunan Jaruma Dr.Girema saratu kwana casa'in da Angonta Hotunan Jaruma Dr.Girema saratu kwana casa'in da Angonta Hotunan Jaruma Dr.Girema saratu kwana casa'in da Angonta

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button