Labarai

Yadda aka sauya rigar ɗakin Ka’aba da sabuwa mai darajar N2.7bn

Advertisment

Ɗakin Kaaba ya samu sabuwar riga wato Kiswah, bayan da aka sauya waccan ta da, an dai kashe dala miliyan 6.5 (N2.7bn) wajen ɗinka sabuwar rigar wacce aka saka ta a safiyar wannan Asabar ɗin.

BBC Hausa ta rahoto cewa an fara aikin sauya rigar tun cikin daren Juma’a bayan Sallar Isha’i zuwa asubahin ranar Asabar, wanda ya zo daidai da ranar 1 ga watan Muharram na shekarar 1444 A.H.

Sabuwar rigar Ka’aba na da nauyi matuƙa

An kiyasata cewa sabuwar rigar nauyinta ya kai kilogram 850, kuma a yanzu ta kasance riga mafi tsada irin ta a duniya.

Ka'aba
Yadda aka sauya rigar ɗakin Ka’aba da sabuwa mai darajar N2.7bn Hoto daga Haramain Sharifain.

Wannan dai shi ne karon farko da ake sauya rigar ɗakin Ka’aba (Kiswah)wato kamar yada ake kiran rigar, a ranar 1 ga watan Muharram.

Kafin wannan lokaci ana sauya rigar ɗakin Kaaba ne a lokacin da ake gudanar da aikin Hajji, musamman a safiyar 9 ga watan Dhul Hijjah idan alhazai sun tafi hawan Arafa.

An bayyana dalilin canja lokacin sanya sabuwar rigar

A ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abdul Rahman Al-Sudais da ke kula da manyan masallatan biyu mafiya daraja a duniya, ya ce an sauya lokacin sauya rigar Kaaba ne bisa sabbin dokoki da shawarwari masarautar Saudiyya.

Mutane sama da 200 ne dai kafofin yada labarai suka rahoto cewa ne suka yi aiki akan rigar Kaaba, tun daga wajen ɗinkata har zuwa sanyata a jikin ɗakin Kaaba. LH na wallafa

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button