Hotuna: Jerin azzaluman mata 8 da aka taba yi a tarihin duniya da irin muguntarsu
A wannan labarin za ku ji labarin jerin azzaluman mata da aka taba yi a tarihi, hotuna, sunaye, tarihi da nau’in muguntarsu kamar yadda shafin Unkown Facts na Facebook ya ruwaito.
- 1. Mary I ‘yar kasar Ingila
An fi saninta da Bloody Mary. Ta halaka rayukan masu zanga-zanga da dama yayin da take kokarin tabbatar da Katolika a Ingila a zamaninta.
Dokar da ta kakaba ce ta sanya aka babbaka masu zanga-zanga wurin 300 wadanda aka zarga da tayar da tarzoma.
Sai dai abin ban takaicin shine yadda ba doka bata yi aiki akanta ba duk da ta’addancin da ta jagoranta. Sai dai bayan ta mutu, an rushe tsarin katolikan da ta gina.
- 2. Aileen Wuornos
Ita ce ‘yar fashin babban titin da ake zargin ita ce mace ta farko a irin ta’addancinta a kasar Amurka. Ta harba sannan ta yi wa kusan maza 7 fashi da makami a Florida. Kuma ta yi zamani ne a 1980 da doriya zuwa farkon 1990 da doriya.
Kuma tana cewa ne duk wanda ta harba ta yi yunkurin kare kanta da kanta ne. Sai dai daga baya aka kama ta dumu-dumu da laifin halaka maza 6 sannan aka gurfanar da ita gaban kotu.
A shekarar 2002 ne aka yanke mata hukuncin kisa ta hanyar yi mata allurar guba. Bayan shekara daya ne aka bayyana tarihinta a wani fim wanda yayi fice mai suna “Monster” wanda ya bayyana muguntar ta.
- 3. Myra Hindley
Myra ce matar da a tarihin Birtaniya ba a taba mace mai muguntar ta ba. Tare da dan uwan harkallarta, Ian Brady, a shekarar 1960 doriya ne ake hayarsu don halaka jama’a.
Tare suka hada kai wurin yin garkuwa, cutarwa da azabtar da yara 5. Bayan an kama su, Hindley bata nuna alamar nadama ba sannan take yanke ta musanta aikata laifukan.
Kusan shekaru 20 ta dauka tana musanta laifukan. Sai dai a shekarar 1987 ne ta bayyana cewa ta aikata duk laifukan da ake zarginta dasu. A shekarar 2002 ta mutu a gidan yari.
- 4. Karla Hamolka
Ita ce mafi shu’umanci a makasa da aka taba yi a kasar Canada. Ta taimakawa mijinta, Paul Benardo wurin yiwa mata 3 fyade, cikin matan har da kanwarta.
An yanke mata hukunci akan duk laifukan da ta aikata. Bayan ta yi shaida akan mijinta, an rage mata daurin da aka yi mata zuwa shekaru 12.
Da farko Harmolka ta ce mijinta ya dade yana cutar da ita kuma ya tilasta mata aikata duk laifukan da ta yi. Sai dai daga bisani an ga wani bidiyo wanda ya tabbatar da cewa da son ranta ta aikata duk laifukan.
- 5. Rosemary West
A Birtaniya ta yi fice kwarai akan laifukanta. Ita da mijinta sun keta haddin mata dayawa tare da halaka su da kuma birne su a cikin gidansu.
A cikin wadanda su ka aikatawa hakan har da diyarsu, Heather. Tun bayan kama su, West ya musanta aikata laifukan, sai dai mai shari’ar ya kula da akasin hakan.
A shekarar 1995 ne aka kamata da laifin keta haddin mata kusan 10 inda aka yanke mata hukuncin daurin rai da rai.
- 6. Elizabeth Bathory
A cikin littafin tarihi na duniya na Guinness, Elizabeth ce macen da ta fi ko wacce mace yawan kisa a duniya. An kama ta da laifin kisa keta haddi da cutar da mata kudan 650 a tsakanin shekarar 1585 zuwa 1610.
Duk da dai ba a samu kwararan shaidu ba dangane da kashe-kashen da tayi, bata taba shiga gaban coci ba saboda matsayin nasabar da ta fito.
An samu rahoto akan yadda take wanka da jinin mutanen da ta halaka duk don kada ta tsufa.
- 7. Katherine Knight
An haifeta a ranar 24 ga watan Oktoban 1955, kuma har yanzu tana gidan yari don an yi mata daurin rai da rai. Ita ce mace ta farko a Australiya da aka taba yiwa daurin rai da rai.
Ta cutar da masoya kwarai kamar yadda tarihi ya bayyana. Ta cire hakoran tsohon mijinta sannan ta yanka makogwaron wuyan karen mijinta a gaban idonsa.
- 8. Irma Grese
Asali gadi take yi a sansanin Auschwitz, Ravensbrük da kuma Bergen-Belsen. An mayar da ita Auschwitz inda ta zama babbar mai kula da ayyuka a gidan yari. Akwai firsinoni mata fiye da 30,000 da take kula dasu.
A cikin muguntar da tayi har karnuka masu fama da yunwa ta dinga jefawa mazauna kurkukun tare da azabtar da wasu da harbin wasu.
Ta dinga dukan fursunonin da yi musu nau’o’i daban-daban na azaba. Tana matukar jindadin azabtar da fursunoni. Shafin LH na wallafa