Labarai

‘Yan Sanda Sun Cafke Saurayin Da Ya Yi Sata A Gidan Surikansa A Katsina

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta cafke Abdullahi Umar dan shekara talatin da daya, dan asalin garin Kari a karamar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna bisa zargin satar kayayyakin sanya wa a gidan su yarinyar shi da ya zo bakunta.

'Yan Sanda Sun Cafke Saurayin Da Ya Yi Sata A Gidan Surikansa A Katsina
Abdullahi Umar

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya yi baje-kolinsa a helkwatar rundunar da ke cikin garin Katsina.

A lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, Abdullahi Umar ya ce mun hadu da ita a kafar sada zumunci ta Facebook, na ce mata zan zo Katsina ta ce in zo, na shirya na zo, ta tarbe ni hannun bibiyu, na kwana biyu a dakin yayanta, cikon na ukku da zan tafi na sace na’urar mai kwakwalwa ta laptop da hulunan sa ukku da kayan sawa. Na shiga gudan dakin na dauki takalman sawa kafa ukku, a cewarsa. Ya Ubangiji yatsaremu da aikin da nasani amin

WANI LABARIN : Mutanen Gari Sun Kori Wani Mutum Tare Da Ɗiyarsa Bayan Da Aka Lura Cewa Yana Lalata Da Ita

Jama’ar gari sun kori wani mutum daga garinsu bayan ganin yana lalata da ɗiyarsa ta cikinsa bayan an tambayeta kuma ta bayyana gaskiya, a yayin da ta ke zantawa da manema labarai.

Dama tun farko an kori Amaechi Agnalasi da ɗiyarsa, Queen Bassey daga garin Nnobi da ke jihar Anambra bayan gano su na lalata da juna har sun haifi yara biyu.

Mutanen Gari Sun Kori Wani Mutum Tare Da Ɗiyarsa Bayan Da Aka Lura Cewa Yana Lalata Da Ita
Mai Gidan da anka kora shida ‘yarsa

Ta bayyana yadda mahaifin na ta ya dinga lalata da ita kuma ya sanya ta tayi alƙawarin ba za ta sa ke kula wani ba sai shi.

Yayin da aka turke shi don ayi masa tambayoyi, Amaechi ya ce ya tilasta ɗiyarsa ta yi masa rantsuwa saboda ba ya so ta bar shi.

Ya ce sauran yaransa sun gudu sun barshi, wannan dalilin ne yasa ya yi hakan don kada Queen ta bar shi, shi yasa ya fara lalata da ita a yanzu haka ma muna da yara biyu. Yace yanzu yana kallon yaran da suka haifa ne a matsayin ƴaƴan sa, kuma jikokinsa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button