Shin Da Gaske Dss sun Kama Sheikh Bello Yabo Sokoto?
Yanzu nake karanta labari da ake yadawa a Facebook cewa jami’an tsaro DSS sun kama babban Malamin Musulunci, dodon marassa gaskiya da miyagun Shugabanni a Nigeria Sheikh Bello Yabo Sokoto (H)
Kafin nayi nayi wannan rubutun; sai da na kira daya daga cikin manyan Daliban Malam Ballo Yabo inda ya tabbatar min da cewa DSS ba su kama Malam ba, yanzu haka Malam yana gida cikin iyalansa yana shirin karatun da zai gabatar yau, don haka labarin kamashi ba gaskiya bane.
Abinda ya faru wasu suke cewa an kama Malam shine, a karatun da Malam ya gabatar jiya, ya caccaki Kakakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wato Garba Shehu wanda yace bidiyon da masu garkuwa da mutane suka fitar suna dukan mutanen da suka kama wai farfagandace
To shine Malam Bello Yabo Sokoto ya mayarwa Garba Shehu zazzafan raddi a jiya, har yayi fatan Allah Ya sa masu garkuwa da mutanen su cafke Garba Shehu su kaishi sansani su masa duka, daga nan sai ace bidiyon Farfagandace yaji inda dadi
Sheikh Bello ya tabbatar da Garba Shehu a matsayin daya daga cikin mutanen da suke cin amanar shugaba Buhari ta hanyar boye masa gaskiyar abinda yake faruwa
Na saka bidiyo a YouTube channel dina zaku kalli Malam Bello Yabo yadda ya yiwa Garba Shehu ba*kar addu’ah da wankin babban bargo ta wannan link ????
Tabbas duk wanda ya saurari maganganun zai ji a ransa cewa da kyar idan ba’a tura hukuma sun kama Malam Bello ba
Muna rokon Allah Ya tsare mana rayuwar Malam Bello Yabo, Allah Ya kara masa taimako da nasara da cikakken kariya
Daga Datti assalafy