Labarai

Mambobi miliyan 2 mu ka yi wa rijista a Borno — NNPP

Advertisment

Jam’iyar adawa ta NNPP ta ce ta yi wa mambobi da magoya baya sama da miliyan biyu rajistar jam’iyyar a Jihar Borno. Daily Nigerian na ruwaitoMambobi miliyan 2 mu ka yi wa rijista a Borno — NNPP

Shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Borno, Mohammed Mustapha ne ya shaida hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN a Maiduguri a jiya Lahadi.

Shugaban ya ce yanzu jam’iyyar na samun karbuwa sosai a Jihar.

Mohammed ya ce sun shirya tsaf domin su ba sauran jam’iyyu mamaki a dukkan zabukan da ke tafe a 2023.

Advertisment

Ya ce, “Mun tsayar da ’yan takara a dukkan mukamai a Jihar Borno, kuma muna da shugabanni tun daga matakin mazaba har zuwa Jiha wadanda za su wayar da kan masu zabe.

“Ban da dan takararmu na Shugaban Kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, muna da dan takarar Gwamna da na Sanatoci guda uku da na ’yan Majalisar Wakilai guda 10 da kuma na Majalisar Jiha guda 28 a Borno.

“Mun shirya tsaf domin ba ragowar jam’iyyu mamaki da mambobinmu da magoya baya sama da miliyan biyu,” inji Shugaban.

Mustafa ya kuma jinjina wa Hukumar Zabe ta Kasa, INEC saboda kara wa’adin sabunta rajistar zabe, inda ya yi kira ga al’ummar Jihar, musamman matasa da su shiga a dama da su.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button